“Kada Ka Jira Har Sai Sun Fara Jefe Ka”: Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Gargadi Ga Tinubu

“Kada Ka Jira Har Sai Sun Fara Jefe Ka”: Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Gargadi Ga Tinubu

  • An bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi nazari sosai kan tattalin arzikin Najeriya don hana zanga-zangar da ke tafe
  • Primate Elijah Ayodele ne ya yi wannan kira, inda ya koka da cewar kasar na fuskantar rashin jin dadi da yunwa saboda manufofin Tinubu na baya-bayan nan
  • Malamin ya jaddada bukatar shugaban kasa ya gaggauta daukar matakin, yana mai cewa masu karbar albashi ma ba su tsira ba a cikin wahalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya sake tuntubar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ayodele ya gargadi Shugaban kasa Tinubu
“Kada Ka Jira Har Sai Sun Fara Jefe Ka”: Fitaccen Malamin Addini Ya Gagarumin Gargadi Ga Tinubu Hoto: Osho Oluwatosin, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Osho Oluwatosin ya saki, malamin ya bukaci shugaban kasar da ya magance matsin tattaklin arziki da yan Najeriya ke fuskanta a kasar.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

Abun da zai faru idan Tinubu bai magance wahalar ba

A cikin sanarwar, Primate Ayodele ya gargadi Tinubu da ya magance halin da tattalin arzikin kasar ke ciki saboda yana kara tabarbarewa a kullun, rahoton Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar malamin addinin, za a yi gagarumin zanga-zanga idan shugaban kasar bai magance matsalolin da ke tunkarar kasar ba.

Ya bayyana cewa mutane na fama da yunwa kuma masu karbar albashi ma basa iya rike kansu da abun da suka samu, rahoton PM News.

"Kada ka jira sai sun fara jifanka da duk yan wani dan siyasa kafin ka yi aiki, ya kamata ka yi wani abu yanzu," in ji shi.

Gwamnan PDP zai sauya sheka, Inji Ayodele

A wani labarin kuma, mun ji cewa Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa nan ba da jimawa ba Fasto Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom, zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi babban burin Tinubu kan talakawan Najeriya, ya roki 'yan kasar kan hakuri

Gwamna Eno jigo ne a jam’iyyar PDP, jam’iyyar da ta kai shi ga samun nasara a zaɓen 2023 da ya gabata.

Da yake bayyana hasashen nasa ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), Ayodele, wanda ya kafa cocin INRI Evangelical Spiritual, ya tabbatar da cewa "PDP za ta yi asarar Akwa Ibom".

Asali: Legit.ng

Online view pixel