NUC Ta Fitar da Cikakken Jerin Sunayen Jami'o'in da Aka Haramta a Najeriya

NUC Ta Fitar da Cikakken Jerin Sunayen Jami'o'in da Aka Haramta a Najeriya

  • Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta saki jerin sunayen haramtattun makarantun jami'o'i a kasar
  • Mukaddashin sakataren NUC, Chris Maiyaki, ya ce hukumar ta gano akalla jami'o'i 37 da basa bisa ka'ida a Najeriya
  • Maiyaki ya bayyana cewa hukumar ta kama wasu mutane kuma ta sanya DSS ta shiga cikin rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Hukumar Jami’o’i ta Kasa (NUC), ta gano wasu haramtattun jami’o’i 37 da ke aiki a fadin kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Mukaddashin sakataren NUC, Chris Maiyaki, ya ce hukumar ta kama wasu mutane da laifin gudanar da jami'o'i ba bisa ka'ida ba a Najeriya.

NUC ta kama wasu masu tafiyar da haramtattun jami'o'i
NUC Ta Fitar da Cikakkun Jerin Sunayen Jami'o'in da Aka Haramta a Najeriya Hoto: NUC
Asali: Facebook

Maiyaki ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Channels TV a Abuja a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yi wa Sadiya Farouk tambayoyi kan zargin karkatar da N37bn a gwamnatin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren na NUC ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) na da hannu wajen dakile ayyukan haramtattun makarantu a kasar.

Ya bukaci iyaye da su duba shafin NUC don ganin haramtattu da halastattun jami'o'i a Najeriya domin gudun fadawa tarkonsu.

NUC ta saki jerin sunayen haramtattun jami'o'i
Jerin haramtattun jami'o'i
Asali: UGC

Jerin jami'o'in da za a dakatar da digirinsu

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa yayin da ake fama ƙaruwar jami'o'i masu bayar da digirin bogi a Afirika, gwamnatin Bola Tinubu ta ce za a ƙara sanya takunkumi ga ƙasashe kamar Kenya, Uganda, da Jamhuriyar Nijar.

Hakan ya biyo bayan dakatar da tantancewa da amincewa da takardun shaidar digiri daga Jamhuriyar Benin da Togo bayan wata fallasa da ta tona asirin wasu jami'o'i a Cotonou.

Ministan ilmi na Najeriya, Tahir Mamman, ya bayyana matsayar gwamnatin tarayya kan Kenya da Uganda yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a yammacin Laraba, 3 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke Halima Shehu shugabar hukumar NSIPA bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da ita

Matashi ya mallaki digiri da N600k

A gefe guda, Umar Shehu Audu ɗan jaridar da ya bankaɗo hanyar samun digirin bogi na Kwatano, ya yi ƙarin haske kan hanyoyin da yabi ya samu kwalin digirin.

Umar Audu wanda yake aiki da jaridar Daily Nigerian ya dai bi wasu hanyoyi inda ya samu kwalin digiri daga wata jami'a a Jamhuriyar Benin, ba tare da ya taɓa shiga aji ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel