Minista Ya Fadi Abin da Yake Hana Bola Tinubu Iya Barci da Kyau a Aso Rock Villa

Minista Ya Fadi Abin da Yake Hana Bola Tinubu Iya Barci da Kyau a Aso Rock Villa

  • Tunji Alausa ya kaddamar da wani gini da aka yi a asibitin tarayya na FMC da ke Ebutte Meta a jihar Legas
  • Karamin Ministan lafiya ya yi jawabi inda ya ce Bola Tinubu ya damu da yadda kayan asibiti suke kara tsada
  • Dr. Alausa ya yi maganar yunkurin da ake yi da kuma cigaba da aka samu a wajen yaye ma’aikatan jinya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Karamin Ministan lafiya, Tunji Alausa ya ce Bola Ahmed Tinubu ya damu da yadda wasu abubuwa su ke faruwa a Najeriya.

Dr. Tunji Alausa ya ce irin tashin farashin magunguna da karancin muhimman magunguna su na ba shugaban Najeriyan ciwon kai.

Bola Tinubu
Magunguna sun kara tsada a zamanin Bola Tinubu Hoto: @ilufemiloyei, @NGRPresidency
Asali: Twitter

Hankalin Bola Tinubu ya tashi

Kara karanta wannan

"Kada ka jira har sai sun fara jefe ka": Fitaccen malamin addini ya yi gagarumin gargadi ga Tinubu

Punch ta rahoto Ministan kiwon lafiya yana cewa tsadar magunguna da kayan asibiti na cikin abubuwan da ake kokarin gyarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya damu da yadda manyan kamfanonin hada magunguna ke ficewa daga kasar.

Kamfanoni sun bar Najeriya

A baya an ji yadda manyan kamfanoni kamar GlaxoSmithKlin su ka tattara su ka fice.

Jaridar ta ce Biode Pharmaceuticals, Barewa Pharmaceuticals, Toki Linkworld, Nigeria Hoechst da Evans Medical Plc sun tashi.

Sauran kamfanonin da su ka bar Najeryiya su ne: Welcome, Phoenix da kamfanin UTC.

A dalilin haka, farashin magunguna ya tashi kamar yadda wani masani a harkar ya yi wa Legit bayani da mu ka tuntube shi a baya.

Bola Tinubu ya bude ginin FMC

Da yake jawabi wajen kaddamar da sabon ginin asibitin FMC a Ebutte Metta a jihar Legas, ya ce shugaban kasa ya yi maganar batun.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

Pulse ta rahoto Ministan yana cewa shugaba Tinubu ya ba ma’aikatar lafiya ta duba yadda za a rage tashin farashin kayan magunguna.

Alausa ya kuma ce zuwa karshen shekarar nan, za a rika yaye malaman jinya 120, 000.

Siyasar Kano sai Kano

Idan aka koma siyasa, an ji yadda kotun sauraron korafin zabe da kotun daukaka kara su ka tsige Abba Kabir Yusuf, aka ba APC nasara.

Tun ana yi wa magoya bayan Nasiru Yusuf Gawuna kallon rudaddu, yanzu labarin ya canza a Kano yayin da ake jiran hukuncin kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel