Ku Raba Mana Shinkafar Tinubu Yanzu, Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Fadawa Yan Majalisa

Ku Raba Mana Shinkafar Tinubu Yanzu, Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Fadawa Yan Majalisa

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta caccaki yan majalisa kan kin raba kayan abincin da suka samu daga wajen Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Babban daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce ya kamata yan majalisar tarayya su fara rabawa mutanen mazabunsu kayan abincin
  • Akintola ya ce kungiyar kare hakkin musulmi ba za ta daina caccakar yan majalisar ba har sai sun raba kayan abincin da suka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci Sanatoci da yan majalisar wakilai da su fara rabon buhuhunan shinkafa da sauran kayan abincin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rarraba masu.

Babban daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce sanatoci 109 sun samu kayan abincin da ya kai naira miliyan 200 yayin da yan majalisa 360 suka samu wanda ya kai naira miliyan 100 kowannensu.

Kara karanta wannan

"Kada ka jira har sai sun fara jefe ka": Fitaccen malamin addini ya yi gagarumin gargadi ga Tinubu

MURIC ta caccaki yan majalisa
Ku raba mana shinkafar Tinubu yanzu, Kungiyar kare hakkin musulmi ta fadawa yan majalisa Hoto: @GregMil66046993
Asali: Twitter

Akintola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a shafin MURIC na yanar gizo a ranar Juma'a, 5 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Koda dai an ga wani dan majalisa daga Edo a wani bidiyo da ya yadu yana nuna rumbun ajiya cike da dubban buhuhunan shinkafa, har yanzu wasu sanatoci da yan majalisa suna karyata cewar sun karbi kayan tallafi daga wajen shugaban kasar.
"Ta yaya dan majalisa daya ya fito ya nunawa mutanen mazabarsa dubban buhuhunan shinkafa yayin da sauran suka yi gum? Ta yaya yan majalisar wakilai suka yarda cewa sun karbi kayan tallafi masu yawa yayin da sanatoci suka karyata karbar komai? Shin majalisar dattawa cike take da masu zagon kasa da rudani?"

Akintola ya zargi wasu daga cikin ‘yan majalisar da haifar da rudani, ya kuma ce suna yunkurin yin banza da kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin da jama’a ke ciki.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Kungiyar kare hakkin musulmin ta bukaci shugabannin majalisar dattawa da ta wakilai da su yi magana da kuma magance matsalar.

MURIC ta yi kira ga yan majalisar da suka samu tallafin da su gaggauta fara rabon su a tsakanin mazabarsu.

Akintola ya yi kira ga yan Najeriya da su yi hakuri yayin da ‘yan majalisar ke tantance kayan.

"MURIC na son tabbatar wa yan Najeriya cewa ba za mu daina caccakar yan majalisar ba har sai sun raba abin da suka karba."

Malamin addini ya gargadi Tinubu

A wani labarin kuma, Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya sake tuntubar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Osho Oluwatosin ya saki, malamin ya bukaci shugaban kasar da ya magance matsin tattaklin arziki da yan Najeriya ke fuskanta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel