Manyan Labarai A Yau
Manufofin gwamnatin tarayya na fuskantar barazana saboda beraye. Olatunbosun Oyintiloye ya nunawa Tinubu tulin kudi, ya bada shawarar hattara da barayi.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta aike da sakon gayyata zuwa ga ministar jin kai da yaki da fatara, Betta Edu.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara. Hatsarin motan wanda ya ritsa da wasu motoci biyu ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 10 har lahira.
Dakarun sojojin sama na Operation Hadin Kai sun salwantar da rayukan tantiran yan ta'addan Boko Haram bayan sun yi musu luguden wuta ta sama a jihar Borno.
Za a kashe makudan kudi da sunan gyare-gyare a majalisar tarayya. Face-face, gyare-gyare da ‘yan kwaskwarima a nan da can za su ci Biliyoyin kudi a majalisar.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da fara bincike kan badakalar biyan N585.2m zuwa wani asusu, domin bayar da tallafi ga marasa galihu a wasu jihohin kasar nan.
Wasu daga cikin wadanda tsohon shugaban Muhammadu Buhari ya nada mukamai na fuskantar bincike daga gwamnatin Shugaba Tinubu ta hannun hukumar EFCC.
Hukumar NSIPA ta ce ministar jin kai da kawar da talauci, Betta Edu bata da hannu a kowani irin hada-hadar kudi ko zartar da hukunci a cikin hukumar.
Tsohon ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, ya kare gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ngige ya ambato ayyukan da Buhari ya yi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari