Betta Edu: Hukumar EFCC Ta Dauki Muhimmin Mataki Bayan Tinubu Ya Dakatar da Ministar Jin Kai

Betta Edu: Hukumar EFCC Ta Dauki Muhimmin Mataki Bayan Tinubu Ya Dakatar da Ministar Jin Kai

  • Dakatacciyar ministar jin ƙai da yaƙi da fatara, Betta Edu, ta samu gayyata daga hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC
  • Gayyatar na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita bisa zarge-zargen da ake mata na aikata ba daidai ba
  • Tuni shugaban ƙasan ya bayar umarnin gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi wa dakatacciyar ministar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) ta gayyaci ministar harkokin jin kai da yaƙi da fatara, Betta Edu, zuwa hedikwatar ta da ke unguwar Jabi a babban birnin tarayya, Abuja.

Gayyatar na zuwa ne ƙasa da mintuna 30 bayan shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya sanar da dakatar da Edu daga ofis ta hannun mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Tinubu ya dakatar da minista 1 daga aiki nan take, ya bai wa EFCC sabon umarni

Hukumar EFCC ta gayyaci Betta Edu
Hukumar EFCC ta aike da sakon gayyata zuwa ga Betta Edu Hoto: Economic and Financial Crimes Commission, Betta Edu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust tace wani wani jami’in hukumar EFCC ya tabbatar mata da aike wa da saƙon gayyatar zuwa ga Betta Edu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa tun da farko hukumar ta bayar da shawarar dakatar da ministan cikin gaggawa domin share fagen binciken da shugaban ƙasa ya bayar da umarnin a gudanar.

Majiyar ya yi nuni da cewa, nan take hukumar ta dauki matakin fara aiki kan umarnin gudanar da cikakken bincike bisa zargin biyan kuɗin tallafin N585.189m da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas zuwa wani asusu.

Meyasa EFCC ta gayyaci Betta Edu?

Majiyar ya bayyana cewa:

"Binciken da muke yi kan zargin biyan kuɗin ba zai gudana yadda ya kamata ba idan ba mu ba da shawarar dakatar da ministan ba. Dakatar da ita zai ba mu ƴancin yin aikinmu sosai kamar yadda shugaban ƙasa ya umarce mu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci a yi bincike kan kudin tallafin talakawa N37bn da aka sace a ofishin Betta Edu

"Tuni aka aike mata da takardar gayyata a hukumance. Muna tsammanin za ta girmama gayyatar don ba da haske mai kyau game da zargin. Don haka muna sa ran zuwanta nan ba da jimawa ba."

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun hukumar EFCC ba, Dele Oyewale, saboda layukan wayarsa a kashe su ke.

EFCC Ta Cafke Halima Shehu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta cafke Halima Shehu, dakatacciyar shugabar hukumar NSIPA.

Kamun da hukumar ta yi wa Halima na zuwa ne bayan Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da ita kan badaƙalar N3bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel