Gwamnatin Tinubu Ta Fara Binciken Minista Kan Badakalar N585.2m

Gwamnatin Tinubu Ta Fara Binciken Minista Kan Badakalar N585.2m

  • Binciken gudanar ba daidai ba ya iso kan ma'aikatar jin ƙai da yaƙi ɗa fatara ƙarƙashin jagorancin Betta Edu
  • Hakan na zuwa ne bayan ministar ta bayar da umarnin a fitar da N585.2m na tallafin marasa galihu na wasu jihohi huɗu zuwa wani asusu
  • Bayo Onanuga, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike kuma za a ɗauki matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta ce tana binciken fitar da kuɗin tallafin naira miliyan 585.189 da aka ware wa marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas zuwa wani asusu.

Wannan dai na zuwa ne zo ne yayin da wasu ƙungiyoyin fararen hula suka yi kira da a kori ministar harkokin jin ƙai da kawar da talauci, Dr Betta Edu, saboda ba da umarnin biyan kuɗin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Jerin mutanen da Buhari ya nada mukamai da Tinubu yake bincika ta hanyar amfani da EFCC

Bincike ya iso kan Betta Edu
Fadar shugaban kasa ta fara bincike kan badakalar N585.2m a ma'aikatar jin kai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Betta Edu
Asali: Facebook

Sun roƙi shugaban ƙasa da kada ya amince da ba daidai ba, inda suka buƙaci a tsige Edu daga muƙamin minista, sannan hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su yi mata tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara bincike kan badaƙalar N585.2m

Jaridar Daily Trust ta ce mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya shaida mata cewa ana bincike kan lamarin.

Onanuga ya ƙara da cewa:

"Bayan binciken za a ɗauki matakin da ya dace."

A cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Betta Edu, kuma aka miƙa wa ofishin Akanta-Janar na tarayya, Edu ta ba da umarnin a fitar da Naira miliyan 585.189 zuwa wani asusu na wata mai suna Bridget Mojisola Oniyelu.

Takardar da aka bankado ta bayyana cewa an biya kuɗin a asusun Oniyelu.

Betta Edu Ta Nesanta Kanta da Badaƙalar N3bn

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya yi Allah wadai da hare-haren yan bindiga, ya sha muhimmin alwashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministar harkokin jin ƙai da yaƙi da fatara, Dr Betta Edu, ta ce ba ta da alaƙa da almundahanar Naira biliyan 3 da aka yi a hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA).

Edu ta bayyana sanya ta a cikin almundahanar N30bn a matsayin ƙarya wacce kuma ba ta da tushe ballantana makama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel