‘Yan Majalisa Sun Sake Ware Wani Naira Biliyan 30 Domin Gyare-Gyaren Ginin Majalisa

‘Yan Majalisa Sun Sake Ware Wani Naira Biliyan 30 Domin Gyare-Gyaren Ginin Majalisa

  • A shekarar nan ta 2024 da aka shiga, ana so a kashe makudan kudi da sunan gyare-gyare a majalisa
  • Naira biliyan 30 aka sake warewa domin a gyara majalisar tarayya, bayan biliyoyin da za a kashe a albashi
  • Bayanai sun nuna har yau ba a iya kammala ayyukan da aka fara a majalisar kasar a shekarun baya ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - ‘Yan majalisa sun ware karin N30bn da nufin a gyara zauren majalisar tarayya a cikin kundin kasafin kudin 2024.

Rahoton da aka samu daga Punch dazu ya ce wadannan biliyoyi na cikin N344.85bn da ake sa ran majalisar za ta batar a bana.

Majalisa
Za ayi gyaran Majalisa a kan N30bn Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Za a gyara majalisa a kan N60bn?

Kara karanta wannan

Shinkafar Naira Biliyan 57 da Tinubu ya raba ya tona asirin Sanatoci da ‘Yan Majalisa

A maimakon N197.93bn, an ji ‘yan majalisa sun kara kasafinsu zuwa N344.85bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin kudin shekarar nan da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu shi ne mafi yawa a tarihin gwamnatin tarayya.

Idan aka kashe kudin, hakan yana nufin an batar da N60bn a kan gyare-gyare da kwaskwarima a ginin zauren majalisa.

Aikin gyare-gyaren majalisa ya ki karewa

A shekarar bara, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce shugaban kasa zai kaddamar da ayyuka a majalisar kasar.

Jaridar ta rahoto Sanata Akpabio ya ce ayyukan da ake yi a majalisar za su ci N30bn, a lokacin an sa rai za a gama a Disamba.

An yi ta dakatar da lokacin kammala aikin daga Agustan 2022 zuwa Junairun 2023, har aka koma Disamba, ga shi ba a gama ba.

Me ya hana a gama gyaran majalisa?

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

‘Yan kwangila sun shaida cewa ba laifinsu ba ne da aikin bai je ko ina ba, su ka zargi gwamnati da kin bada kudin kwangilar.

Da zarar an saki kudi, kamfanin da ke aikin ya nuna a shirye su ke su kammala komai, Nairaland ta fitar da rahoton nan.

Da kwamitin majalisar dattawa ya kai masu ziyara, wani Injiniya Tajudeen Olanipekun ya ce karyewar Naira ya kawo cikas.

Hukumar FCDA ta bakin Richard Nduul ta ce an ba kamfanin Messrs Visible Construction Nigeria Limited da ke aikin N19bn.

Jawabin shugaban kasa da aka shiga 2024

Duk da matsalolin da ake fuskanta, ana da rahoto Bola Tinubu ya nuna da gaske yake yi wajen cin ma burinsa a shekarar bana.

Shugaba Tinubu zai dage wajen ganin talaka ya samu sauki, ya yi alkawari zai yi wa ma’aikatab gwamnati karin albashi a 2024

Asali: Legit.ng

Online view pixel