Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dabara 1 Da Ta Dauko Domin Karya Farashin Abinci a 2024

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dabara 1 Da Ta Dauko Domin Karya Farashin Abinci a 2024

  • Gwamnatin tarayya ta nuna aniyarta na magance tashin farashin kayan masarufi a fadin kasar
  • Daya daga cikin matakan da gwamnati ke shirin cimmawa shi ne na tallafa wa manoma domin kara yawan noman shinkafa
  • Sabbin bayanai daga Hukumar Kididdiga ta Kasa sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci a halin yanzu ya kai kololuwa cikin shekaru 18

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gwamnatin tarayya ta fara noman kayan amfanin gona mai yawa a kokarinta na karya farashin kayayyakin abinci a fadin kasar.

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 5 ga watan Janairu a jihar Jigawa.

Gwamnatin tarayya ta fara kokarin karya farashin kayan abinci
Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dabara 1 da Ta Dauko Domin Karya Farashin Abinci a 2024 Hoto: Nurphoto
Asali: Getty Images

A cewar Kyari, abinci na daya daga cikin manyan damuwar gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya umarci a yi bincike kan kudin tallafin talakawa N37bn da aka sace a ofishin Betta Edu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamansa:

"Muna da shirye-shirye don tabbatar da samar da abinci mai yawa ta yadda za a samar da abinci ga kasar daidai da ajandar shugaban kasa kan tsaron abinci.
"Haka kuma, muna da niyyar samar da kayayyaki da yawa domin sauko da farashin kayan abinci da suka hau.
“Wannan ya kasance ne saboda a yau, abu na farko da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki a cikin tattalin arzikin kasa shine hauhawar abinci. Don haka muna so mu yi aiki tukuru don samar da su da yawa.
“Shugaban kasa ya ba mu tallafin da muke bukata kuma za mu kammala shi, inda za mu fara da noman shinkafa.”

Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa ministan ya kuma bayar da lokacin da za a fara wannan shiri tare da yin tsokaci kan lokacin da yan Najeriya za su fara ganin saukar farashin kayan abinci.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

"Tuni muka fara shirin. Cikin mako uku masu zuwa, ya kamata komai ya kammala."

Farashin kayan abinci a Najeriya

Hukumar Kididdiga ta Kasa ta saki rahotonta na farashin kayan masarufi a Nuwamba 2023 cikin watan Disamban 2023, wanda ke nuni da cewa Najeriya ta samu karuwar farashin kayan abinci, inda ya kai kashi 32.84%, mafi girma cikin shekaru sama da 18.

Da yake magana kan ko farashin abinci zai ragu nan ba da jimawa ba, bisa ga dimbin shirin noma na gwamnati, Kyari ya kara da cewa:

“Ya dogara ne akan karfin kasuwa na wadatar kayayyaki da bukatu. Don haka idan muka kara samar da kayayyaki, tabbas zai yi tasiri.”

Ya jaddada cewa gwamnati na kokarin samar da karin kayayyaki, domin hakan zai yi tasiri sosai kan tsadar kayan abinci a fadin kasar nan ba da dadewa ba.

A halin da ake ciki, bincike ya nuna cewa ana sayar da buhun shinkafa akalla a kan naira 95,000.

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

Legit Hausa ta tuntubi wasu yan Najeriya kan wannan tanadi da gwamnatin tarayya ke yi don jin yadda suka karbi batun.

Malama Amina Kolo ta ce:

“Muna fatan da gaske gwamnati take domin gaskiya tura ta kai bango, yanzu kowa mabukaci ne a kasar nan, albashin wata baya kai mu ko’ina saboda tsadar rayuwa. Babu ranar da za ka je kasuwa baka ji an kara farashin abubuwa ba. Shinkafa yar gida mai dan kyau idan baka da N1400 toh ba za ka sameta ba, haba ina zamu da wannan al’amari.”

Malama Zainab Momi kuwa cewa ta yi:

“Mun sha jin irin haka, kullun ace talaka zai sha jar miya amma kukan ma da wuya ake shanta. Ban taba ganin tsadar rayuwa irin ta wannan lokaci ba. Yanzu fa komai sai dai yar dabaru ake yi ana cin abinci amma ba wai koshi ake yi ba. Cewa na yi rannan na gaji da shinkafa mai tsakuwa, koda na tambayi shinkafa yar waje sai ce mun aka yi N2200 ne kwano, haka na hakura na siya tamu ta gida. Ya kamata gwamnati ta duba wannan abun.”

Kara karanta wannan

Ku raba mana shinkafar Tinubu yanzu, Kungiyar kare hakkin musulmi ta fadawa yan majalisa

Bankin duniya ya yi hasashe kan Najeriya

A gefe guda, mun ji a baya cewa babban Bankin Duniya ya bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyakin masarufi da karancin habakar tattalin arziki a Najeriya zai kara jefa mutane miliyan 2.8 cikin talauci nan da karshen shekarar 2023.

Wannan bayanin ya biyo bayan wani rahoto mai taken, ‘Nazarin habakar talauci: Bincike da hasashe a kasashen da ke tasowa na duniya,’ wanda aka fitar kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel