Cikakken Jerin Ranakun Hutun da Yan Najeriya Za Su Mora a Shekarar 2024

Cikakken Jerin Ranakun Hutun da Yan Najeriya Za Su Mora a Shekarar 2024

Baya ga tunawa da muhimman ranaku da bukukuwan tarihi, ranakun hutu na ba ƴan Najeriya damar shaƙatawa da morewa yayin hutu daga aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng ta jero ranakun hutun shekarar 2024, domin taimaka muku wajen tsara shekarar yadda ya kamata.

Ranakun hutu a shekarar 2024
Yan Najeriya za su samu hutu a shekarar 2024 Hoto: BENSON IBEABUCHI/AFP, Emmanuel Osodi/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Hutun sabuwar shekara: 1 ga watan Janairu

A ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, aka yi hutun ranar sabuwar shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hutun ya taimaka wa ƴan Najeriya samun hutu daga aiki yayin da suka tsallaka daga 2023 zuwa 2024.

Hutun Good Friday: 29 ga watan Maris

A shekarar 2024, hutun Good Friday zai kasance a ranar Juma'a, 19 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Gwamna Bello ya tsige sarakuna 3 daga karagar mulki, ya yi muhimmin garambawul

Good Friday rana ce ta hutun mabiya addinin Kirista domin tunawa da gicciye Yesu Almasihu da rasuwarsa.

Hutun Easter: 1 ga watan Afrilu

Hutun Easter na shekarar 2024, zai kama ne a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu.

Bikin Easter biki ne na Kirista da ke murna da tashin Yesu Almasihu daga matattu. Yana faruwa kwana uku bayan mutuwar Yesu a ranar Good Friday.

Hutun ƙaramar Sallah: 10 ga watan Afrilu

An ƙiyasta cewa ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu ne za a yi bikin ƙaramar Sallah na shekarar 2024.

A lura cewa ganin jinjirin watan Shawwal ne zai tabbatar da ko ranar za ta kasance ranar Idi ko a'a.

Ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu kuma na iya zama ranar Idi.

Ranar ma'aikata ta duniya: 1 ga watan Mayu

Ranar Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, ita ce ranar ma'aikata ta duniya. Ana kuma kiranta da 'Labour Day' ko 'May Day'.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

Ana bikin ranar ma'aikata a kowace shekara a ranar 1 ga Mayu don tunawa da gwagwarmaya da sadaukarwar da ma'aikata ke yi.

Ranar Dimokuraɗiyya: 12 ga watan Yuni

Bikin ranar dimokuradiyya wani biki ne mai matuƙar muhimmanci ga Najeriya domin ya nuna irin ci gaban da ƙasar ta samu wajen gudanar da mulkin dimokuraɗiyya.

A ranar Laraba 12 ga watan Yuni ne gwamnatin Najeriya za ta ayyana hutun domin ba ƴan kasar damar tunawa da yadda ƙasar ta koma kan turbar dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Hutun Babbar Sallah: 17 ga watan Yuni

Ana iya yin bikin babbar Sallah a ranar Litinin, 17 ga watan Yunin 2024. Sai dai, ya danganta da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah.

Ranar Talata, 18 ga watan Yuni, na iya zama ƙarin hutun babbar Sallah. Hakan ya biyo bayan kammala aikin Hajjin bana.

Hutun Mauludi: 16 ga watan Satumba

A ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, gwamnatin tarayya za ta bayar da hutun Mauludi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Atoni-janar a jihar Arewa ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 81

Ranar ita ce ranar da aka keɓe domin tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Ranar samun ƴancin kan Najeriya: 1 ga watan Oktoba

Ranar Talata 1 ga watan Oktoba ne ranar da Najeriya ta samu ƴancin kai, ita ce ranar da aka keɓe domin murnar samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya.

Ranar Kirsimeti: 25 ga watan Disamba

Laraba, 25 ga watan Disamba, ita ce za ta kama ranar Kirsimeti. Kirsimeti bikin kiristoci ne domin tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.

Ranar Dambe (Boxing Day): 26 ga watan Disamba

Ranar dambe ita ce ranar bikin da ake yi washegarin ranar Kirsimeti.

A al'adance ana yin bikin ne a Burtaniya da wasu ƙasashe rainon Burtaniya (Commonwealth), waɗanda suka haɗa har da Najeriya.

Sauran ranaku masu muhimmanci a cikin 2024

Baya ga ranakun da aka bayyana a sama, akwai kuma wasu muhimman ranakun da za a yi bukuwansu a cikin 2024, sai dai gwamnati ba za ta ayyana hutu ba domin su.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gawar gwamnan APC da Allah ya yi wa rasuwa ta iso Najeriya, Hotuna sun bayyana

Waɗannan ranakun sun haɗa da:

Ranar masoya (Valentine) da Ash Wednesday: 14 ga watan Fabrairu

Ranar Laraba 14 ga watan Fabrairu ita ce ranar masoya. Ranar St Valentine, wacce ta samu sunanta daga Saint Valentine, wani limamin Katolika da ya rayu a Roma a ƙarni na uku, biki ne na shekara-shekara don soyayya, abota da ƙauna.

Haka kuma ranar 14 ga watan Fabrairu kuma za ta zama ranar 'Ash Wednesday'.

Ranar na ɗaya daga cikin shahararrun ranaku masu tsarki da muhimmanci a kalandar mabiya ɗarikar Katolika.

Ranar mata ta duniya: 8 ga watan Maris

Ranar Juma'a 8 ga watan Maris ita ce ranar mata ta duniya. Rana ce ta duniya da ake bikin murnar nasarar da mata suka samu a zamantakewa, tattalin arziƙi, al'adu da siyasa.

Haka kuma ranar ta yi kira da a ɗauki matakai domin kara ƙaimi wajen samar da daidaiton mata.

Ranar Yara: 27 ga watan Mayu

Kara karanta wannan

Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

A ranar Litinin 27 ga watan Mayu ne Najeriya za ta yi bikin ranar yara. An ƙirƙiro ranar a matsayin ranar biki a shekarar 1964 kuma ranar hutu ce ga yaran makarantun firamare da sakandare.

Gwamna Bago Ya Ba da Hutun Kwana 7

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya ayyana hutun kwanaki bakwai ga ma'aikatan jihar.

Gwamnan ya bayar da hutun ne domin ma'aikatan su samu damar gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin tsanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel