Manyan Labarai A Yau
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, ya aike da wasika zuwa ga hukumar da'ar ma'aikata kan dalilinsa na kin amsa gayyatar da aka yi masa.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilin tashin abin fashewa a birnin Ibadan a jihar Oyo. Gwamnan ya ce laifin masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne.
Bankunan Access, First Bank da Zenith na daga cikin bankunan da ke da albashin ma'aikata mafi tsoka a watanni tara na farkon 2023 har zuwa shekarar 2024.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin yin amfani da ilmi domin ganin ya kawo karshen matsalar rashin tsaro da aka dade ana fama da ita a kasar nan.
Al'ummar garin Ibadan sun shiga zullumi sakamakon kara da girgiza da aka ji biyo bayan tashin wani abin fashewa da wasu ke zargin tukunyar gas ne ko bam.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi martani kan kiran da aka yi a kwnakin nan ga jam'iyyun adawa su yi hadaka domin kawar da ita a zaben 2027.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta ta addabi kasar nan, shugaban kasar ya ce ba zai huta ba har sai ya ga karshenta.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran manyan baki sun halarci bikin kaddamar da sabon littafi domin karrama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro ta yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ta addabi ƙasar nan.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari