Manyan Labarai A Yau
Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan kisan gillar da yan bindiga suka yi wa daya daga cikin yan mata shida yan gida daya da suka sace a birnin tarayya Abuja.
Kotun Koli ta yi hukunci kan wasu kararrakin zabubbukan gwamnonin da aka kora a kotun daukaka kara. Kotun ta sauya hukuncin da kotun daukaka kara ta yi.
Gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia, ya mika kokon bararsa ga yan bindiga bayan sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Ukum ta jihar.
Buba Galadima wanda jigo ne a jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya bayyana cewa alkalan Kotun Koli sun tsira da suka tabbatar da nasarar Gwamna Abba.
Masu garkuwa da mutane sun tafka sabuwar ta'asa da rashin imani a birnin tarayya Abuja. Miyagun mutanen dai sun halaka mutum hudu da suka yi garkuwa da su.
Daya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya, Adebayo Ogunlesi, ya zama daya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya da na Afirka bayan ya mallaki dala biliyan 2.3.
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan karar da dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Rivers, kan zaben Gwamna Fubara na PDP.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) za ta sake bincikar wasu tsofaffin gwamnoni 11 da ke zargi da badakalar makudan kudade.
Jam'iyyar APC ta shirya zaben shiga takarar majalisa, amma hatsaniya ta biyo baya. ‘Dan Takara ya kawo kara ga Abdullahi Ganduje yayin da rikicin tikiti ya barke.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari