Shugaba Tinubu Ya Fadi Hanya 1 da Zai Bi Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Fadi Hanya 1 da Zai Bi Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai yi amfani da ilmi domin ganin matsalar rashin tsaro ta kawo ƙarshe
  • Shugaba Tinubu ya kuma yi Allah wadai da yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane da ƴan bindiga ke yi a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin magance matsalar sace-sace da hare-haren ƴan bindiga da ta addabi ƙasar nan ta hanyar amfani ɗimbin ilimi.

Tinubu wanda ya yi Allah-wadai da hare-haren, ya bayyana su a matsayin abin tayar da hankali, rashin tsoron Allah, da kuma mugun nufi.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana abin da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, ya fadi mafita

Shugaba Tinubu ya fadi hanyar magance rashin tsaro
Shugaba Tinubu ya yi alkawarin yin amfani da ilmi don kawo karshen rashin tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ya yi wannan alƙawari ne a lokacin da ya karɓi baluncin tawagar Jam’iyyatu Ansaridden ta Harkar Musulunci a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman Cif Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata.

Tinubu ya ce yayin da jami’an tsaro ke aiki da gaggawa domin tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta, nan ba da daɗewa ba za a fitar da duk wani abu, manufofi da tsare-tsare da ake buƙata domin bunƙasar ilimin matasan Najeriya.

Wacce hanya Tinubu zai bi don magance rashin tsaro?

Ya ƙara da cewa ilimi shi ne maganin matsalolin da ke tada hankalin al’umma, inda ya ƙara da cewa makamin talauci shi ne ilimi.

A kalamansa:

"Babu wani makamin yaƙi da talauci da yake da ƙarfi kamar ilmi.

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin kisan Nabeeha yan bindiga sun sace daliban jami'a a Katsina

"Ina tabbatar muku cewa mun zo nan ne domin mu canja rayuwar mutanenmu. Mun zo nan don inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali, da wadatar tattalin arziƙi.
"Mun himmatu wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa tare da mai da hankali kan ilimin yaranmu. Za mu sa malamanmu su shiga harkar ilimi wanda zai dace da makomar ƙasar nan. Yana da muhimmanci. Ilimi ya kawo ni da addu'o'in ku da taimakon ku. Idan babu ilimi, babu abin da zai samar da fata ga ƴan Adam.
"Ku fara yin addu'o'i na musamman. A fara samar da ingantaccen ilimi ga matasan mu. Garkuwa da mutane da fashi ba hanyar Allah ba ce. Zubar da jinin juna abu ne mai muni.
"Kuma ba za a samu ci gaba ba idan babu zaman lafiya. Da zaman lafiya ne kawai za mu iya kawar da talauci. Dole ne mu himmatu wajen samar da zaman lafiya domin tattalin arziƙinmu ya inganta."

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi abu 1 da zai faru da alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba ya yi rashin nasara

Shugaba Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro na ƙasa.

Shugaban ƙasan ya gana da hafsoshin tsaron ne a fadarsa da ke Abuja yayin da matsalar tsaro take ƙara taɓarɓarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel