Shugaba Tinubu Ya Fusata Kan Matsalar Rashin Tsaro, Ya Sha Sabon Alwashi

Shugaba Tinubu Ya Fusata Kan Matsalar Rashin Tsaro, Ya Sha Sabon Alwashi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalar rashin tsaro a ƙasa da ke ƙara taɓarɓarewa
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ba zai huta ba har sai ya kawo ƙarshen duk wasu masu hannu kan matsalar rashin tsaron
  • Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi wajen ƙaddamar da littafin da aka rubuta domin karrama tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai an kawar da “wakilan duhu" masu haddasa rashin tsaro a ƙasar nan gaba ɗaya.

Tinubu yayi magana ne a ranar Talata, 16 ga watan Janairu a wurin ƙaddamar da littafi mai suna "Working With Buhari, Reflections Of a Special Adviser, Media and Publicity (2015-2023)", cewar rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi hanya 1 da zai bi wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya

Shugaba Tinubu ya yi magana kan rashin tsaro
Shugaba Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Femi Adesina, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya rubuta littafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana game da gwamnatin Buhari, Tinubu ya ce tsohon shugaban ƙasar ya hau mulki ne a shekarar 2015 a cikin matsalolin tattalin arziƙi da rikicin Boko Haram.

Me Tinubu ya ce kan matsalar rashin tsaro?

Shugaban ya ce ƴan Najeriya ba za su iya mantawa da yadda sojoji suka yi yaƙi da Boko Haram a ƙarƙashin Buhari tare da kwato yankunan ƙasar nan ba.

A kalamansa:

"A wani lokaci, da alama har Abuja, fadar gwamnati, za ta fada hannun ƴan Boko Haram tare da tayar da bama-bamai a ginin Majalisar Dinkin Duniya, Banex Plaza, Nyanya da sauran wurare a cikin Babban Birnin Tarayya.
"Ba za mu iya mantawa da yadda sojojin mu suka yi artabu da ƴan ta’addan Boko Haram a ƙarƙashin jagorancin shugaba Buhari don ƙwato mana yankunanmu da tura su tafkin tafkin Chadi inda ba su da wata barazana ga ƴancin kanmu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana dalili 1 da ya sa Buhari ba zai iya tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar ba

"Dole ne in ce aikin tabbatar da tsare kowane yanki na ƙasarmu bai ƙare ba. Gwamnatina za ta kawar da ragowar ƴan Boko Haram, Ansaru, ƴan fashi da masu garkuwa da mutane. Ba za mu huta ba har sai kowane wakilin duhu ya kafe gaba ɗaya."

Atiku Ya Magantu Kan Rashin Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa talauci da yunwa ke sanyawa rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel