Zaben 2027: APC Ta Yi Martani Kan Kiran Pat Utomi na Hadakar PDP, NNPP da LP Don Kawar da Ita

Zaben 2027: APC Ta Yi Martani Kan Kiran Pat Utomi na Hadakar PDP, NNPP da LP Don Kawar da Ita

  • An yi watsi da yunƙurin haɗewar jam'iyyun adawa masu ƙarfi domin kawar jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Kakakin jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana cewa matakin ba zai taɓa yiwuwa ba idan har Farfesa Pat Utomi ne ya ƙaddamar da shi
  • Wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa da ke rajin haɗewar sun haɗa da Labour Party (LP), New Nigerian Peoples Party (NNPP) da Peoples Democratic Party (PDP)

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta mayar da martani kan kiran da aka yi na haɗakar manyan jam’iyyun adawa domin ƙwatar mulki a hannunta a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Babban jigon jam’iyyar Labour Party, Farfesa Pat Utomi, ya sha alwashin tattaunawa da shugabannin jam’iyyun adawa domin su ajiye burinsu a yi haɗaka.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi abu 1 da zai faru da alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba ya yi rashin nasara

APC ta yi martani kan Pat Utomi
APC ta yi martani kan kiran Pat Utomi na yan adawa su yi hadaka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Pat Utomi
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa babban abin da manyan jam’iyyun adawa za su mayar da hankali a kai a 2027 shi ne kafa babbar jam’iyyar siyasa da za ta ƙwace mulki daga hannun APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran Pat Utomi na yin haɗaka

A cikin bayanin da ya yi a baya-bayan nan, Utomi ya bayyana cewa:

“Na ce da su (ƴan takarar jam’iyyun adawa), ba batun ku ba ne, a’a batun Najeriya ce, na talakawan da ke bakin titi ne, magana ce da gaske ta yadda za a fita daga wannan sana’ar ta raba ƴan canji daga kuɗin sayar da mai zuwa yadda za mu iya zama ɗaya daga cikin mafi kyawun tattalin arziki."

A halin da ake ciki, wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Felix Morka, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, ta bukaci jama’a da su guji ɗaukar Farfesa Utomi da muhimmanci.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotun koli Shugaba Tinubu ya fadi muhimmin abu 1 da yake so gwamnonin APC su yi

Ya bayyana cewa matakin Utomi ya kasance tuni ne da shekarar 2021 lokacin da ya ba da irin wannan shawara amma "bai wuce kanun labarai ba."

Shirin Kafa Sabuwar Jam'iyyar Adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Pat Utomi ya bayyana cewa ya tattauna da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso domin ƙafa sabuwar jam'iyya.

Ana shirin kafa sabuwar babbar jam'iyyar ne domin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng