Jerinsu: Bankuna 11 da Suka Fi Biyan Ma'aikatansu Albashi Mai Tsoka a 2023, Access Bank Na Gaba

Jerinsu: Bankuna 11 da Suka Fi Biyan Ma'aikatansu Albashi Mai Tsoka a 2023, Access Bank Na Gaba

  • A cikin watanni tara na farkon shekarar 2023, bankunan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Access Holdings da FBN Holdings sun ƙara albashin ma’aikata da kaso 33%
  • Manyan bankunan na Najeriya sun ƙara yawan albashin ma’aikatan ne don rage tasirin tsadar rayuwa
  • Sauran bankunan da ke cikin jerin sun haɗa da bankin Zenith, UBA, GTBank, da bankin Fidelity, da dai sauransu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Access Holdings da FBN Holdings sun biya mafi girman albashin ma’aikata idan aka kwatanta da sauran bankunan kasuwanci a cikin watanni tara na farkon 2023.

A cikin bayanan da suka fitar na baya-bayan nan, bankuna 11 na Najeriya sun ƙara yawan kuɗaɗen da suke biyan ma'aikatansu.

Bankunan da ke biyan albashi mai tsoka
Bankunan suna ba ma'aikatansu albashi mai tsoka Hoto: Dan Barko
Asali: UGC

A cewar ƙididdigar kuɗi na bankuna 11 da ke a kasuwar hada-hadar kuɗi ta Najeriya, ma'aikatan bankin Access sun samu ƙarin kuɗaɗen da suka kai N117.6bn a watanni tara na farkon 2023 daga N89.8bn na watanni taran farko a 2022.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar CCB? Gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, ma'aikata a First Bank sun samu ƙari zuwa N113.2bn daga N84.9bn na baya.

Manyan bankunan Najeriya masu yawan albashin ma’aikata

Kuɗaden da ake kashewa ma'aikata da suka shafi albashi da jin daɗi na wani lokaci, sun haɗa da albashi, da sauran abubuwa irinsu inshorar lafiya, fansho da horaswa.

A cewar jaridar Businessday, ƙididdigar kuɗaɗen bankunan ta nuna cewa bankin UBA ne ya kashe adadi na uku da ya kai N111.1bn, sai kuma Zenith da ya kashe N88.4bn, Stanbic IBTC mai N45.9bn, GTBank mai N37.6bn da FCMB mai N34.0bn.

Sauran bankunan sun haɗa da Bankin Fidelity mai N30.3bn, bankin Wema mai N19.0bn, bankin Sterling mai N16.3bn, da bankin Unity mai N10.3bn.

Adadin kuɗaɗen da bankunan ke kashewa ya karu da kaso 33% cikin 100% a cikin shekara guda, inda bankin Zenith da UBA suka samu ci gaban da ya kai kaso 43.9% cikin 100% da kaso 37.6% a duk shekara.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana abin da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, ya fadi mafita

Arzikin Dangote Ya Karu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dukiyar attajirin da yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ta ƙaru.

Dangote ya samu wannan tagomashin ne na N514bn bayan matatar man fetur ɗinsa ta fara aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel