Manyan Labarai A Yau
Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa kan zargin cin hanci.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar fitacciyar jarumar masana'antar fina-finai ta Kannywood, Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Daso. Ta rasu a ranar Talata.
'Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun fara tuntubar mahukuntan matatar man fetur ta Aliko Dangote kan farashin da ya kamata a sayar da man a kasuwa.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ya unurci a tsare babban jami'in kamfanin Binance a gidan gyaran hali na Kuje.
Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Edo daga kan mukaminsa. An tsige Philip Shaibu ne kan wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Babban bankin Najeriya (CBN) ya sallami wasu daga cikin ma'aikatansa har guda 50 a ci gaba da garambawul din ake yi a bankin. Akwai wasu da za a kora nan gaba.
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami'anta sun hallaka 'yan ta'adda mutum shida a jihar Borno. An kashe su ne bayan sun yi wa sojoji kwanton bauna.
Wasun 'yan bindiga sun kai farmaki a gidan dan majalisar wakilan tarayya a birnin Makurdi na jihar Benue. A yayin harin sun tafka barna mai tarin yawa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi martani kan kalaman da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi a kan gwamnatinsa na cewa ta gaza.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari