Manyan Labarai A Yau
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da samun nasarar ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka miyagun 'yan bindiga mutum biyar.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan farmaki a jihar Kogi inda suka hallaka mutane da dama tare da kona gidaje masu tarin yawa a yayin harin.
Hukumar Alhazai ta kasa( NAHCON) ta sanar da yawan maniyyatan Najeriya da zau gudanar da aikin Hajjin bana a shekarar 2024. Ta ce sama da mutum 50,000.
Basussukan waje da jihohin Najeriya suka ciyo a shekarar 2023 ya karu da kaso 3.36% daga wanda suka ciyo a shekarar 2022. Jihohi 10 na kan gaba a jerin.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno, ta sanar da samun nasarar cafke wasu mutum hudu da ake zargi da yunkurin kona wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar.
Wani jami'in rundunar ƴan snada da ke aikin raka jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya rasu ana tsaka da tafiya, fasinja ya bayyana yadda lamarim ya auku.
Jam'iyyar APC a jihar Ribas ta zargi gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da kitsa yadda zai haramta majalisar dokokin jihar domin cimma wata manufa.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi sababbin nade-nade guda biyar a gwamnatinsa. Daga ciki akwai na shugaban hukumar kula da harkokin majalisar dokokin jihar.
An samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar Gamboru da ke cikin birnin Maiduguri na jihar Borno. Jami'an 'yan kwana-kwana sun yi nasarar kashe ta.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari