'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Dan Majalisa Har Cikin Gida a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Dan Majalisa Har Cikin Gida a Jihar Arewa

  • Ƴan bindiga sun nemi sa'ar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabun Logo-Ukum-Katsina Ala a jihar Benuwai
  • Tsagerun sun kai farmaki a gidansa wanda yake a cikin birnin Makurdi, babban birnin jihar a ranar Asabar, 6 ga watan Afirilun 2024
  • Sai dai, ba su tarar da shi a gidan ba amma sun yi ɓarna tare da sace kayayyaki masu amfani bayan sun yi wa mai gadin gidan dukan tsiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benuwai - Ƴan bindiga sun kai farmaki a gidan ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Logo-Ukum-Katsina Ala, Solomon Wombo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙarshen mako a gidan ɗan majalisar wanda yake a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace dalibai a Arewa sun bayyana kudin fansan da za a ba su

'Yan bindiga sun kai hari a Benue
'Yan bindiga sun kai hari gidan dan majalisa a Makurdi Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa ɗan majalisar ya tabbatar mata da aukuwar lamarin ta wayar tarho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka kai harin

An tattaro cewa ƴan bindigan su huɗu sun dira gidan ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar, 6 ga watan Afrilun 2024.

Hayaniyar da mai gadin gidan ya ji lokacin da suke ƙoƙarin shigowa ta sanya shi fitowa, sai dai sun yi masa barazana da cewa kada ya yi ihu.

Sun tambayi inda ɗan majalisar yake amma sai mai gadin gidan yace ba ya nan. Sun kuma buƙaci mabuɗin shiga cikin gidan, amma mai gadin sai mai gadin ya tabbatar musu da cewa ɗan majalisar ya tafi da shi.

Hakan ya fusata maharan inda suka yi wa mai gadin dukan kawo wuƙa ƙafin su fice daga gidan.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fadi kokarin da zai yi a samu tsaro a jihar Zamfara

Kafin su bar gidan sai da suka lalata wani ɓangare tare da sace duk wani abu mai amfani da suka ci karo da shi.

An bayyana cewa jami'an ƴan sanda na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Jaridar Naija News ta ce ɗan majalisa mai wakiltar Katsina Ala a majalisar dokokin jihar, Bemdoo Peter Ipusu ya yi Allah wadai da harin.

Ƴan bindiga sun hallaka manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun halaka manoma biyu tare da jikkata wasu da dama a jihar Benuwai.

Maharan sun yi ajalin manoman ne yayin da suka kai farmaki ƙauyen Onipi da ke ƙaramar hukumar Otukpo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel