Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Gidado (Daso) Ta Rasu

Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Gidado (Daso) Ta Rasu

  • Allah ya yi wa shahararriyar jarumar masana'antar fina-finai ta Kannywood, Saratu Gidado Daso rasuwa
  • Marigayiyar ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Talata, 9 ga watan Afirilun 2024 bayan ta kammala sahur
  • Daso kafin rasuwarta ta yi suna sosai a masana'antar fina-finan inda ta kwashe sama da shekara 18 tauraruwarta na haskawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Allah ya yi wa fitacciyar jarumar Kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso rasuwa.

Jaridar Leadership ta ce an samu labarin rasuwar marigayiyar ne a ranar Talata, 9 ga watan Afrilun 2024.

Saratu Gidado Daso ta rasu
Allah ya yi wa Saratu Gidado rasuwa Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

Ƴan uwanta sun ce Daso ta rasu ne a cikin barcinta da sanyin safiyar Talata bayan ta kammala Sahur.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Daso, an sanar da mutuwar wata matashiyar jarumar fina-finai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ya tabbatar da rasuwar marigayiyar a shafinsa na Facebook.

Yaushe za a yi jana'izar Saratu Daso?

Daso ta yi fice a masana’antar fina-finan Kannywood inda ta kwashe sama da shekaru 18. Za a yi jana'izar ta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a yau Talata.

Daso ta yi fice a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood sama da shekara 18. Kafin ta yi fice a harkar wasan kwaikwayo, Saratu ta yi aiki a matsayin malamar makaranta.

Daso wacce ta rasu tana da shekara 56 an haife ta ne a ranar 17 ga watan Janairu, 1968 a cikin birnin Kano.

Ta yi fice musamman a rawar da take takawa a fina-finai ta matsayin uwa da mace mai faɗa.

Ta fara fitowa a cikin fim a shekarar 2000 a wani fim mai suna Linzami Da Wuta, wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bi sahun Tinubu, ya kara ranakun hutun Sallah a jiharsa

Sauran fitattun fina-finan da suka haska tauraruwar marigayiyar sun haɗa da Nagari, Gidauniya, Mashi, da kuma Sansani.

Jarumar Kannywood ta rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa, Fatima Sa'id wacce ke fitowa a matsayin Bintu a shirin Dadinkowa ta riga mu gidan gaskiya.

Jarumar ta rasu ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu sakamakon rashin lafiyar da ta yi fama da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel