Rundunar Sojoji Ta Dauki Mataki Kan 'Yan Ta'addan da Suka Farmaki Jami'anta a Borno

Rundunar Sojoji Ta Dauki Mataki Kan 'Yan Ta'addan da Suka Farmaki Jami'anta a Borno

  • Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da hallaka ƴan ta'adda shida da suka farmaki jami'anta a jihar Borno
  • Ƴan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne inda suka hallaka Laftanar ɗaya tare da raunata wasu sojoji huɗu
  • Biyo bayan aukuwar lamarin an aika da ƙarin jami'ai inda suka yi artabu da ƴan ta'addan tare da fatattakarsu daga maɓoyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe ƴan ta’adda shida da suka kashe jami’anta a hanyar Biu-Buni-Yadi, a jihar Borno.

Ƴan ta'addan dai sun farmaki jami'an sojojin ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna a kan hanyar.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Sojoji sun sheke 'yan ta'adda a jihar Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Rundunar ta ce bayan aukuwar lamarin, an aika da ƙarin sojoji inda suka tarwatsa maɓoyar ƴan ta'addan a cikin Timbuktu Triangle, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace dalibai a Arewa sun bayyana kudin fansan da za a ba su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me rundunar sojoji ta ce kan lamarin?

Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Edward Buba, shi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ya ce Laftanar guda ɗaya kawai aka kashe a yayin kwanton ɓaunan.

Manjo-Janar Buba, ya ce sauran sojoji huɗu da suka samu raunuka, ana ci gaba da ba su magani a asibiti, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

A kalamansa:

“A ranar 5 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 09:35 na safe, dakarun Operation Hadin Kai, sun fuskanci kwanton ɓauna na ƴan ta'adda a hanyar Buratai-Buni-Yadi.
"Abin baƙin ciki, a yayin fafatawar an kashe Laftanar guda ɗaya. Yayin da wasu sojoji huɗu suka samu raunuka inda ake duba lafiyarsu a asibiti.
"Dakarun sojojin da aka ƙara aikawa sun bi ƴan ta’addan har zuwa maɓoyarsu a cikin Timbuktu Triangle tare da yin musayar wuta."

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru a Delta 'yan ta'adda sun sake yi wa sojoji kwanton bauna, an rasa mutum 6

"Sojojin sun yi nasarar kashe shida daga cikin ƴan ta’addan tare da ƙwato bindigu ƙirar AK 47 guda biyar da harsashi na musamman mai kaurin 7.62mm guda 103."

- Janar Edward Buba

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka tantiran ƴan ta'adda guda uku a jihar Kaduna.

Sojojin sun sheƙe ƴan ta'addan ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna lokacin da suke kan hanyar kai gyaran baburansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel