Rikicin APC: Kotu Ta Bada Umurni Dabam Kan Dakatar da Ganduje

Rikicin APC: Kotu Ta Bada Umurni Dabam Kan Dakatar da Ganduje

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Kano ta jingine umurnin da babbar kotu ta bada na dakatar da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa
  • Kotun ta umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje da kada su yi amfani da umurnin babbar kotun na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje
  • Alƙalin kotun, mai shari'a Abdullahi Liman shi ne ya bada wannan unurnnin bayan buƙatar da lauyan Ganduje ya shigar a gabansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasara a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

Babbar kotun ta jingine dakatarwar da shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, suka yi wa tsohon gwamnan na Kano a makon nan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan umarnin kotu, ta faɗi mutanen da suka dakatar da Ganduje

Kotu ta soke dakatar da Ganduje
Ganduje ya yi nasara a gaban kotu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ganduje: Wane umurni kotun ta bada?

Alƙalin kotun, mai shari’a Abdullahi Liman ya umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, ka da su yi aiki da umurnin babbar kotun jihar na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Abdullahi ya kuma ya hana duk waɗanda umurnin babbar kotun jihar ya shafa bin umurnin, har sai an saurari ƙarar da Ganduje ya shigar ta neman a yi masa adalci a saurari ɓangarensa.

Wannan umurnin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar kotun jihar ta amince da buƙatar shugabannin APC na mazaɓar Ganduje ta dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

Meyasa aka 'dakatar' da Ganduje a APC?

Shugabannin dai sun dakatar da Ganduje ne saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar Ganduje, babban ɗansa ya ba da mamaki a ofishin yaki da cin hanci

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan Afrilu domin sauraren buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje wacce lauyansa Jazuli Mustapha ya gabatar a gabanta.

Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da Abubakar Daudu.

Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan Najeriya, kwamishinan ƴan sandan Kano, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), da hukumar sibil difens (NSCDC)

APC ta magantu kan dakatar da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa har yanzu ba a kawo mata takardar umarnin kotu na dakatar da shugaban jam'iyyar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba.

Abdulkarim Kana mai ba APC shawara kan harkokin shari'a ne ya bayyana haka a babbar sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel