Shugabannin APC Za Su Sanya Labule da Ganduje a Abuja, Bayanai Sun Fito

Shugabannin APC Za Su Sanya Labule da Ganduje a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jamiyyar APC na ƙasa zai samu manyan baki a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Shugabannin jam'iyyar na mazaɓun da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa za su ziyarci Ganduje domin nuna goyon bayansu a gare shi
  • Ziyarar ta su na zuwa ne biyo bayan wasu shugabannin jam'iyyar sun yi ikirarin sanar da dakatar da tsohon gwamnan jihar na Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugabannin mazaɓu na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, za su ziyarci shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje a birnin tarayya Abuja.

Hakan na zuwa ne dai bayan wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar na mazaɓar Ganduje sun sanar da dakatar da tsohon gwamnan na jihar Kano, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

APC ta yi fatali da batun dakatar da Ganduje, ta dauki mataki kan masu hannu a ciki

Shugabannin APC za su ziyarci Ganduje
Shugaban APC, Ganduje zai yi manyan baki a Abuja Hoto: @officialAPCNg
Asali: Twitter

Yaushe 'yan APC za su ziyarci Ganduje?

Shugabannin za su ziyarci Dr. Ganduje ne a ranar Laraba, 17 ga watan Afirilun 2024 domin jaddada goyon bayansu a gare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar wacce aka shirya, za ta gudana ne a sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa da misalin ƙarfe 11:00 na safe, rahoton Naija News ya tabbatar.

Hakan na zuwa ne dai kwana biyu bayan mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a a mazaɓar Ganduje, Halliru Gwanzo, ya ce an dakatar da Ganduje daga jam'iyyar.

Meyasa aka dakatar da Ganduje?

Gwanzo, wanda ya yi magana da ƴan jarida a Kano, ya ce shugabannin jam'iyyar sun ɗauki matakin dakatarwar ne saboda zarge-zargen cin hanci da ake yi wa Ganduje.

Ya kafa hujja da tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa waɗanda gwamnatin jihar Kano ke yi wa tsohon gwamnan inda aka shirya gurfanar da shi a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Sai dai, shugabannin jam'iyyar APC a matakin jiha sun yi fatali da dakatarwar tare da dakatar da Gwanzo da sauran shugabannin jam'iyyar da ke da hannu a lamarin na tsawon watanni shida.

Jam'iyyar APC ta shigar da ƙara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani mai zafi kan dakatar da shugabanta na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar ta shigar da ƙara a gaban babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, kan waɗanda suka kitsa dakatar da Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel