APC Ta Yi Fatali da Batun Dakatar da Ganduje, Ta Dauki Mataki Kan Masu Hannu a Ciki

APC Ta Yi Fatali da Batun Dakatar da Ganduje, Ta Dauki Mataki Kan Masu Hannu a Ciki

  • Jam'iyyar APC ta yi magana kan dakatar da shugabanta na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da aka yi a mazaɓarsa
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ta shigar da ƙara a gaban babban sufeton ƴan sanda na ƙasa domin gudanar da bincike kan lamarin
  • Ta bayyana cewa waɗanda suka sanar da dakatar da Ganduje sojojin gona ne ba ainihin ƴaƴan jam'iyyar ba ne na asali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar APC a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, ta yi magana kan dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar APC ta bayyana dakatar da shugabanta na ƙasa a matsayin labari na ƙarya wanda babu gaskiya a cikinsa

APC ta musanta dakatar da Ganduje
APC ta karyata batun dakatar da Ganduje Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakinta, Felix Morka, jam’iyyar mai mulki a Najeriya ta ce waɗanda suka sanar da dakatar da Ganduje ba ƴan jam'iyyar ba ne.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: 'Yan majalisa sun samo hanyar warware dambarwar da ta dabaibaye jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta shigar da ƙara a kan Ganduje

Jam’iyyar ta bayyana cewa ta shigar da ƙara gaban babban sufeton ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, inda ta buƙaci a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.

Ta kuma buƙaci a hukunta waɗanda suka kitsa wannan aikin tare da waɗanda suka ɗauki nauyinsu.

Idan ba a manta ba dai, Haladu Maigwanjo, mai ba jam’iyyar APC kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Tofa ta jihar Kano, a ranar Litinin, 15 ga Afrilu, ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

Maigwanjo ya ce an dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne domin ba shi damar fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

Me APC ta ce kan dakatar da Ganduje?

Sai dai, a yanzu uwar jam'iyyar ta ƙasa ta soke wannan dakatarwar, inda ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Bayan Matawalle wata kungiya ta caccaki Dattawan Arewa kan sukar Shugaba Tinubu

"Batun dakatarwar aikin wasu masu kutse ne na shugabannin mazaɓa waɗanda ke son kawo ruɗani a mazaɓar Ganduje ta jam'iyyarmu mai zaman lafiya."

Jam'iyyar APC ta yi zargin cewa ƴan siyasar da suka dakatar da Ganduje ba ƴan jam'iyyar APC ba ne a Kano.

Ta bayyana cewa mutanen suna da alaƙa da manyan jami'ai da wakilan jam'iyyar NNPP.

APC tayi hukunci kan dakatar da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ɗauki matakin ladabtarwa kan waɗands suka dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar ta dakatar da su tsawon watanni shida tare da soke matakin da suka ɗauka kan shugaban jam'iyya na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel