Bayan Shekara 10, Sojoji Sun Ceto Wata Cikin 'Yan Matan Chibok da Yara 3

Bayan Shekara 10, Sojoji Sun Ceto Wata Cikin 'Yan Matan Chibok da Yara 3

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sake kuɓutar da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok da aka sace a hannun Boko Haram
  • Lydia Simon ta kuɓuta ne bayan ta tsero daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara inda aka tsare ta na tsawon shekaru masu yawa
  • Ɗalibar wacce ta kwashe shekara 10 a tsare a hannun ƴan ta'addan ta dawo ɗauke da juna biyu na wata biyar da kuma ƴaƴa uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya na Operation Desert Sanity III, Operation Hadin Kai da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas sun ceto wata ɗalibar Chibok, Lydia Simon.

An tattaro cewa, sojojin bataliya ta 82 da ke ƙaramar hukumar Ngoza, sun ceto Lydia ne tare da ƴaƴanta uku a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki hedkwatar ƙaramar hukuma, sun tafka ɓarna

Sojoji sun ceto dalibar Chibok
Sojoji sun sake ceto daya daga cikin 'yan matan Chibok Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A cewar Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Lydia ce ke da lamba 68 a cikin ƴan matan da aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chibok: A ina sojoji suka ceto Lydia?

Ya ce ta tsero ne daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara inda aka tsare ta tsawon shekaru da dama.

Wannan Baiwar Allah mika wuya ga sojojin bataliya ta 82 da ke Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Lydia da aka ceto na ɗauke da juna biyu na wata biyar kuma ta yi iƙirarin cewa ta fito daga garin Pemi da ke Chibok.

Boko Haram: Shekaru 10 da dauke Lydia

A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka cika shekara 10 da sace ƴan mata 276 da mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Jerin lokuta 11 da 'yan ta'adda suka shiga makaranta tare da sace dalibai a Najeriya

Yayin da 57 daga cikin ƴan matan suka kuɓuta bayan ƴan kwanaki kaɗan, daga baya kuma an kubutar da 16, yayin da aka sako 107 a lokuta daban-daban, ta hanyar tattaunawa.

Gwamnati da sojojin Najeriya sun yi alƙawarin ceto sauran ƴan matan da har yanzu suke tsare a hannun ƴan ta'addan.

Ƴan matan Chibok sun dawo da yara

A wani labarin kuma, kun ji cewa da yawa daga cikin ƴan matan Chibok da aka ceto daga hannun Boko Haram sun dawo ɗauke da yara.

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa ƴan mata 21 daga cikin waɗanda aka sako ya zuwa yanzu sun zo gida tare da yara 34.

Asali: Legit.ng

Online view pixel