Hukumar EFCC Ta Ayyana Tsohon Gwamna a Matsayin Wanda Take Nema Ruwa a Jallo

Hukumar EFCC Ta Ayyana Tsohon Gwamna a Matsayin Wanda Take Nema Ruwa a Jallo

  • Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta ɗauki mataki na gaba a ƙoƙarin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi
  • Hukumar yaƙi da cin hancin ta bayyana Alhaji Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan zargin almundahanar kuɗi har N80.2bn
  • Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta yi ƙoƙarin cafke tsohon matashin gwamnan amma lamarin ya faskara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Hukumar na neman Yahaya Bello ne bisa laifukan da suka shafi almindahanar maƙudan kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi barazanar hada-kai da sojoji domin kamo tsohon gwamnan APC

EFCC na neman Yahaya Bello
Hukumar EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo Hoto: EFCC, Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa EFCC take neman Yahaya Bello?

Sanarwar na cewa:

"Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa laifukan da suka shafi almundahanar kuɗi har N80.2bn."
"Duk wanda ke da bayanin inda yake ya kai rahoto cikin gaggawa ga hukumar ko kuma ofishin ƴan sanda mafi kusa."

EFCC ta yi barazana ga Yahaya Bello

A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa hukumar EFCC ta yi barazanar yin amfani da jami'an tsaro na sojoji domin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi.

Barazanar na zuwa ne bayan Yahaya Bello ya ƙi bayyana a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhumen da hukumar ke yi a kansa.

Lauyan EFCC ya bayyana cewa Yahaya bai fi ƙarfin doka, kuma a yanzu ba shi da kariya wacce za ta hana a kamo shi.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

Batun EFCC da binciken Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi kira ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi ɗa'a ga doka kuma ya miƙa kansa ga EFCC domin a gudanar da bincike.

Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, SAN, ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel