Binciken El-Rufai: Jam'iyyar APC ta Bayyana Wanda Take Goyon Baya a Kaduna

Binciken El-Rufai: Jam'iyyar APC ta Bayyana Wanda Take Goyon Baya a Kaduna

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ya bayyana matsayarta kan binciken tsohon gwamnan jihar da majalisar dokokin jihar ke shirin yi
  • Jam'iyyar ta hannun sakataren yaɗa labaranta na jihar ta goyi bayan majalisar inda ta ce ta hanyar binciken ne za a gano gaskiya
  • Hakazalika ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta nuna goyon bayanta kan binciken da za a yi wa gwamnatin tsohon gwamnan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta nuna goyon bayanta kan matakin da majalisar dokokin jihar ta ɗauka na bincikar gwamnatin tsohon Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai.

Binciken dai zai shafi harkokin kuɗi musamman basussukan da tsohon gwamnan ya karɓo domin gudanar da ayyuka lokacin da yake kan mulki.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar Ganduje, babban ɗansa ya ba da mamaki a ofishin yaki da cin hanci

APC ta goyi bayan binciken El-Rufai
APC ta goyi bayan majalisa kan binciken El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta Kaduna, Salisu Wusono, shi ne ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar The Punch ta wayar tarho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salisu ya bayyana binciken a matsayin wani abin farin ciki wanda suke maraba da shi.

Meyasa APC ke goyon bayan binciken El-Rufai?

Sakataren yaɗa labaran na APC ya ce ta hanyar kafa kwamitin binciken za a san haƙiƙanin halin da ake ciki.

“Ina so in tunatar da ɗaukacin ƴan Najeriya cewa jam’iyyar APC ta yi imani da bin doka da oda, haka ma Malam Nasir El-Rufai. Mutum ne mai son bin tsarin jam’iyya.
"Wataƙila gwamnatin da ta shuɗe ta kashe N20m, yayin da mutane ke cewa ya fi ko ya yi kaɗan, kwamitin ne kaɗai zai iya tantancewa tare da faɗawa jama'a haƙiƙanin halin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Binciken El-Rufai: An bayyana dalilin kafa kwamitin bin diddikin ayyukan tsohon gwamnan

- Salisu Wusono

El-Rufai: NLC tana goyon bayan Majalisa

A halin da ake ciki, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta goyi bayan binciken Malam El-Rufai.

Shugaban NLC na Kaduna, Ayuba Suleiman, shi ne ya nuna goyon bayan yayin da ya buƙaci a taɓo batun ma'aikatan da El-Rufai ya kora, cewar rahoton Politics Nigeria.

Ayuba ya ce ƙungiyar ƙwadagon za ta kuma so majalisar ta binciki kuɗaɗen sallamar ma’aikata sama da 32,000 da gwamnatin El-Rufai ta kora ba ta biya ba.

Batun dakatar da El-Rufai daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na dakatar da tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai.

Jam'iyyar ta hannun sakataren yaɗa labaranta ta musanta rahotannin da ke yawo kan cewa tana shirin dakatar da El-Rufai saboda aikata ayyukan da suka saɓawa jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel