Murna Yayin da Dangote Ya Karya Farashin Man Dizal Daga N1200

Murna Yayin da Dangote Ya Karya Farashin Man Dizal Daga N1200

  • Za a samu sauƙi yayin da matatar man hamshaƙin attajirin nan Aliko Dangote ta sanar da sake karya farashin man dizal
  • Sabon farashin na yanzu ya koma N1000 kan kowace lita saɓanin yadda ake siyar da shi a kan N1200 a makonnin da suka gabata
  • Kamfanin matatar man ne ya sanar da karya farashin na dizal a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizal daga N1200 zuwa N1,000 kan kowace lita.

Hakan na ƙunshe ne dai a cikin wata sanarwa da matatar man ta fitar a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilun 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dawo biyan tallafin man fetur, an bayyana kudin da take kashewa

Dangote ya rage farashin dizal
Dangote ya rage farashin man dizal zuwa N1000 Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Kamfanin a cikin sanarwar ya ce rage farashin zai haifar da sauyi mai kyau a dukkanin ɓangarorin tattalin arziƙi tare da rage hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makonni uku da suka gabata, kamfanin ya rage farashin daga kusan N1,600 kan kowace lita zuwa N1,200.

Meyasa Dangote ya rage farashin dizal?

An tattaro cewa rage farashin ba zai rasa nasaba da matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na siyar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida irin su matatar Dangote a Naira ba.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A wani mataki da ba a taɓa ganin irinsa ba, matatar man Dangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizal daga Naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita.
“A yayin da ake fitar da kayayyakin, matatar ta samar da su a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 kan kowace lita makonni uku da suka gabata, wanda ya nuna raguwar sama da kaso 30% cikin 100% na farashin baya na kusan Naira 1,600 kan kowace lita."

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Gombe ta dawo da dokar sharar wata-wata

"Wannan muhimmin ragi na farashin dizal a matatar Dangote, ana sa ran zai haifar da sauyi mai kyau a dukkanin ɓangarorin tattalin arziƙi tare da rage hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan."

Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya kawo mafita domin fita daga ƙangin hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da ita.

Dangote ya ce dole sai farashin baƙin mai ya sauka kafin a yi bankwana da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel