Manyan Labarai A Yau
Rahotanni sun tabbatar da cewa mace mafi tsufa a duniya, Inah Canabarro Lucas ta rasu ta na da shekarƴ 116 a duniya, an tabbatar da mutuwarta ranar Larava.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya miƙa sakok ta'aziyya ga abokiyar aikinsa, Dr. Mariya Mahmoud bisa rasuwar mahaifinta, Alhaji Sani Baban Koko.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa.
Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi kira ga gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, da ya sake tunani kan shirinsa na sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi bayani kan yadda Nyesom Wike ya jawo Peter Obi ya fice daga PDP kafin zaben 2023.
An shiga jimami a jihar Delta bayan rasuwar tsohon gwamnan soja, Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu, ya rasu yana da shekara 84 a duniya. Iyalansa sun fitar da sanarwa.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana cewa nan ba da jimawa James Ibori zai koma jam'iyyar APC. Ya ce sun yi magana tsohon gwamnan kan hakan.
Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu, Abba Moro, ya dora laifi ga Atiku Abubakar kam rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP. Ya ce ya gaza hada kan mambobinta.
Hukumar FCTA ta lalata babura 601 da aka kama a Abuja, Elechi da Abdulateef sun ce hakan na cikin matakin tabbatar da tsaro da hana keta dokokin zirga-zirga.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari