Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Kano ta ba kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar umarnin fitar da kudade domin gyarawa tare da sayo sababbin motoci ga masarautar Kano.
Kungiyar dattawan Zamfara ta nuna damuwa kan ci gaba da muzgunawa wasu daga cikin zababbun 'yan majalisar dokokin jihar. Ta ja kunnen Gwamna Dauda Lawal.
Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya sake jimamin rasuwar Umaru Musa Yar'adua bayan shekaru 15, ya ce marigayin shugaba ne na gari abin koyi.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka mutane a jihar Bauchi. 'Yan bindigan sun kuma yi wa wasu mafarauta kwanton bauna a cikin daji.
Jam'iyyar LP ta samu nakasu a jihar Anambra. Makusancin dan takarar shugaban kasa na LP a zaben 2023, Peter Obi, Oseloka Obaze ya yi murabus daga jam'iyyar.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sanya labule da kamfanonin samar da lantarki na Najeriya. Zaman na su na da nasaba da matsalolin da bangaren ke fsukanta.
Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Adamawa, Humwashin Wonosikou, ya bayyana cewa Gwamna Ahmadu Umaru Finitiri bai da shirin ficewa daga PDP.
An shiga jimami a jihar Plateau bayan samun labarin rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Sonni Gwanle Tyoden. Ya rasu ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya bayyana cewa 'yan Najeriya na shan wahala a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari