Kwana Ya Kare: Babban Jami'i a Gwamnatin Taraba Ya Kwanta Dama a Abuja

Kwana Ya Kare: Babban Jami'i a Gwamnatin Taraba Ya Kwanta Dama a Abuja

  • Babban sakatare a ofishin hulɗa da Abuja na gwamnatin Jihar Taraba, Dauda Maikomo ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya
  • Shugaban ma'aiktan gwamnatin Taraba, Dr. Ahmed Kara ne ya tabbatar da rasuwar a madadin Gwamna Agbu Kefas da safiyar yau Laraba
  • Ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin tare da addu'ar Allah Ya ji kan sa, Ya gafarta masa, Ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure rashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban sakatare a Ofishin Hulɗar Abuja na Gwamnatin Jihar Taraba, Mista Dauda Maikomo, ya rasu a wani asibiti da ke Babban Birnin Tarayya.

Rahotanni sun bayyana cewa Dauda Maikomo ya riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da wata ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Dauda Maikano.
Gwamnatin Taraba ta rasa ɗaya daga cikin manyan sakatarorinta Hoto: Dr. Agbu Kefas
Asali: Facebook

Gwamnatin Taraba karkashin jagorancin Gwamna Agbu Kefas ta tabbatar da rasuwar Maikomo a wata sanarwa da ta fitar, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar Taraba ta yi babban rashi

Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Taraba, Dr. Ahmed Kara ne ya sanar da rasuwar a madadin Gwamna Kefas yau Laraba, 11 ga watan Yuni, 2025

Dr. Ahmed Kara ya ce:

"A madadin Mai Girma Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ina mai sanar da rasuwar Mista Dauda Maikomo, Babban Sakatare na Ofishin Hulɗa da Abuja.
"Dauda Maikomo ya rasu ne a ranar 11 ga Yuni, 2025, sakamakon gajeruwar rashin lafiya.”

Gudummuwar da Maikomo ya bayar a Taraba

Dr. Ahmed Kara ya bayyana mamacin a matsayin jajirtaccen jami’in gwamnati wanda ya bayar da gudunmuwa sosai ga ci gaban Jihar Taraba da ƙasar nan baki ɗaya.

“Jagoranci, hangen nesa, da kuma sadaukarwa da jajircewar da marigayin ke da su za su kasance abin koyi kuma za a yi kewarsa ƙwarai,” in ji shi.

Gwamnatin Kefas ta mika sakon ta'aziyya

Shugaban ma'aikatan ya miƙa sakon ta'aziyya da alhini ga iyalan Marigayi Maikomo, yana mai cewa za su ci gaba da yi masa addu'aur neman gafara.

Dr. Ahmed ya yi addu'ar Allah Ya jikan marigayin kuma ya bai wa iyaƙansa haƙuri da juriyar rashin da suka yi, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Gwamna Agbu Kefas.
Gwamnatin Taraba ta yi alhinin rasuwar Dauda Maikomo Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter
"Allah S. W. A ya jikan marigayi Maikomo, kuma ya ba mu da iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi da muka yi,” in ji Dr. Ahmed Kara.

A ƙarshe, shugaban ma'aikatan ya tabbatar da cewa gwamnatin Taraba za ta karrama marigayin da jana'izar jiha, tana mai cewa za a sanar da rana da lokaci nan gaba.

Mahaifin ministan Buhari ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan Wasanni Wanda ya yi aiki a gwamnatin Buhari, Solomon Dalung tabbatar da rasuwar mahaifinsa ɗan shekara 105 a duniya.

Marigayin mai suna Nimgbak William Fabong Dalung wanda tsohon daraktan lafiya ne ya riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da jinya.

Dalung ya sanar da rasuwar mahaifinsa ne yayin da suke shirye-shiryen birne mahaifiayrsu, wacce ta rasu tana da shekara 90 a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262