Malaman Makaranta
An zargi kamfanin simintin Dangote da rushe makarantar gwamnati saboda hako ma’adanai. Kamfanin Dangote ya rushe makarantar ne ba tare da sanar da hukuma ba.
A sakamakon hukunta jami’ar Baze da majalisar CLE ta yi, wasu sun shiga gagari. Digirin Rotimi Amaechi, Sanata Uba da Dino Melaye na fuskantar barazana.
Gwamntin jihar Neja a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta fito ta yi magana kam rahotannin da ke cewa tana adawa da amfani da Hijabi da mata ke yi.
Allah ya yi wa wata malamar makaranta Misis Oluwatosin Aina rasuwa a jihar Ogun bayan da ta fadi ta ce ga garinku a kusa da motarta tana kokarin zuwa asibiti.
An shiga wani irin yanayi a Jami'ar OAU da ke jihar Osun bayan tsintar gawar lakcara a ofishinsa, marigayin mai suna Dakta Ayo ya mutu a jiya Talata.
Makarantun gwamnati a Legas suka rufe ayyukansu bisa bin umarnin kungiyar kwadago ta NLC. NLC ta bayar da umurni na neman ma’aikata su fara yajin aiki a fadin kasar.
NLC ta bayar da umurnin tsunduma yajin aikin ne a taron majalisar zartarwa na kungiyoyin kwadago na kasa da aka gudanar a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a kokarin ceto jihar daga durkushewa, ya kuma kwace lasisin makarantu masu zaman kansu.
Yayin da ake ci gaba da yajin aikin kungiyar NLC, kungiyoyi da dama sun tsunduma yajin aiki a Najeriya a kokarin bin umarnin kungiyar kwadago ta NLC.
Malaman Makaranta
Samu kari