Gwamna Bala Na Bauchi Ya Bada Umurnin Rufe Makaranta Kan Kisan Wani Yaro

Gwamna Bala Na Bauchi Ya Bada Umurnin Rufe Makaranta Kan Kisan Wani Yaro

  • Gwamna Bala na Bauchi ya ba da umarnin rufe wata makaranta har sai baba ta gani
  • Gwamnan ya ɗauki matakin ne biyo bayan gawar wani yaro da aka tsinta da aka cire wasu sassa na jikinsa
  • Ya umarci jami'an 'yan sandan jihar da su baza komarsu wajen zaƙulo waɗanda suka aikata mummunan aikin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ba da umarnin rufe makarantar da aka tsinci gawar wani yaro mai suna Mohammed Abidin Musa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya je yi wa iyayen yaron da aka kashe jaje da kuma ta'aziyya kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

Gwamnan Bauchi ya ba da umarnin rufe wata makaranta a jiharsa
Gwamnan Bala ya ba da umarnin a rufe wata makaranta a jihar Bauchi Saboda kisan wani yaro. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Gwamnan Bala ya damu kan kisan yaro a makaranta

Gwamna Bala ya nuna damuwarsa matuƙa kan mummunan kisan da aka yi wa yaron wanda bai ji ba bai gani ba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bayyana Abu 1 Da Dole Sai PDP Ta Yi Kafin Ya Mara Mata Baya a Zaben Jihar Bayelsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana kisan a matsayin mummunan laifi abin ƙi, inda ya kuma ba da tabbacin cewa jami'an 'yan sandan jihar na iya bakin ƙoƙarinsu wajen gano wadanda ke da hannu a ciki.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafartawa yaron, sannan kuma ya yi kira ga iyaye da su ƙara sanya idanu a kan yaransu da kewayensu.

Yadda aka tsinci gawar yaron a makaranta

A rahoton da jaridar The Nation ta wallafa, an tsinci gawar Mohammed Abidin ne a cikin mummunan yanayi na cire wasu sassa na jikinsa da aka yi.

Gwamna Bala ya koka kan yadda ake ƙara samun yawaitar ayyuka na ta'addanci a jihar Bauchi, wacce ta kasance hanyar shiga jihohi aƙalla bakwai da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Daga ƙarshe gwamnan ya ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al'ummar jihar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja Ya Fadi Ainihin Abinda Ya Sanya Shi Tattaunawa Da 'Yan Bindigar Jiharsa

Gwamnatin jihar Bauchi ta kulle makarantu 5 saboda cutar mashaƙo

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan rufe wasu makarantu guda biyar da gwamnatin jihar Bauchi ta yi sakamakon rahoton ɓullar cutar mashaƙo da aka yi a cikinsu.

Gwamnatin ta kuma ba da tabbacin cewa za ta rufe duk wata makaranta da aka samu ɓullar cutar ba tare da ɓata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng