Tinubu Ya Amince Da Samar Da Motocin Bas Ga Dalibai, Ya Cire Musu Takunkumin Lamunin Karatu

Tinubu Ya Amince Da Samar Da Motocin Bas Ga Dalibai, Ya Cire Musu Takunkumin Lamunin Karatu

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar da motocin bas don jigilar ɗaliban manyan makarantu
  • Shugaban ya yi hakan ne don ragewa ɗaliban yawan kuɗaɗen da suke kashewa domin zirga-zirga
  • Ya kuma bayyana cewa za a sanya ɗalibai cikin tsarin tallafin kuɗaɗe da abinci da Gwamnatin Tarayya ke shirin bai wa 'yan Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar da motocin bas ga ƙungiyoyin ɗalibai da ke manyan makarantu domin jigilar ɗalibai a ƙasa baki ɗaya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Dele Alake ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin kamar yadda PM News ta wallafa.

Tinubu zai samar da motocin jigilar ɗalibai
Tinubu ya amince da samar da motocin jigilar ɗalibai a manyan makarantu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu zai samar da motocin ne don ragewa ɗalibai wahalhalun zuwa makaranta

Alake ya bayyana cewa Tinubu ya ɗauki wannan matakin ne domin ragewa ɗaliban manyan makarantu wahalhalun da suke sha sanadiyyar cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Boka Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi Layar Zana Ba Yayin Da Masu Garkuwa Suka Zo Sace Shi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce hakan zai taimakawa ɗalibai wajen rage yawan kuɗaɗen sufuri da suke kashewa a zirga-zirgar da suke yi zuwa makarantunsu.

Ya kuma ƙara da cewa hakan zai kuma ragewa iyayen yaran nauyin kuɗaɗen da suke bai wa 'ya'yan na su domin su je makaranta kullum.

Tinubu ya cire takunkumin da aka sanya wa tsarin bashin kuɗaɗen karatu

Alake ya kuma bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cire duk wani takunkumi da ke iyakance waɗanda za su iya cin gaskiyar bashin tallafin karatu.

Ya ce shugaban ya yi hakan ne don bai wa duk wani ɗalibi da yake buƙata ba tare da iyakance waɗanda za su iya amfana da tsarin ba.

Hakazalika, Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin makarantun Gwamnatin Tarayya da su guji ƙarin kuɗaɗen da ake biya ba bisa ƙa’ida ba, domin gudun kar a ƙara wa iyayen yara nauyi na kuɗaɗen da suke kashewa kamar yadda Leadership ta wallafa.

Kara karanta wannan

Stella Okotete: Lauya Ya Bukaci Majalisa Ta Fatattaki Daya Cikin Ministocin Tinubu, Ya Bada Kwakkwaran Dalili

Alake ya kuma ƙara da cewa gwamnatin ta Tinubu na ƙoƙarin ganin ta sanya ɗaliban makarantun cikin tsarin abinci da kuma kuɗaɗe na tallafi da za ta bayar.

Daga ƙarshe ya ba da tabbacin cewa Shugaba Tinubu zai bai wa ɓangaren ilimi muhimmanci sosai a gwamnatinsa, inda ya ce zai inganta hanyoyin walwalar ɗalibai da ma malamansu baki ɗaya.

NEC ta bayyana yadda za a raba kuɗaɗen tallafi ga 'yan Najeriya

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan bayanin da majalisar tattalin arziƙin ƙasa (NEC) ta yi.

NEC ta bayyana cewa, ko wace jiha za ta raba kuɗaɗen tallafin ta hanyar amfani da rajistar al'umma da take da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel