Abba Gida Gida Ya Dakatar Da Shugabannin Makarantu 2 A Kano Kan Wasa Da Aiki

Abba Gida Gida Ya Dakatar Da Shugabannin Makarantu 2 A Kano Kan Wasa Da Aiki

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya umarci dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda biyu
  • An dakatar da shugabannin biyu ne kan rashin kula da aiki da kuma kin zuwa wurin aiki a yau Litinin 11 ga watan Satumba
  • Kwamishinan ilimi a jihar shi ya ba da wannan umarni inda ya bukace su da mika kansu ga ma'aikatar don bincike

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ba da umarnin dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare kan saba doka.

Balarabe Kiru, Daraktan wayar da kan jama'a a ma'aikatar ilimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 11 ga watan Satumba.

Abba Kabir ya dakatar da shugabannin makarantu 2 a Kano
Abba Gida Gida Ya Dauki Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Me yasa Abba Kabir dakatarsu a Kano?

Kiru ya ce lokacin da jami'an kula da makarantu su ka ziyarci makarantar ba su samu shugabannin makarantun ba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Tallafi: Yayin Da Ake Halin Kunci, Matasa Sun Yi Warwason Shinkafa Kan Motoci 3 A Arewa, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce wannan wasa da aiki ne da kuma saba doka, inda ya ce makarantun sun hada da Kwalejin yarukan Sin da Faransa da ke karamar hukumar Madobi a jihar.

Ya kara da cewa sakatariyar din-din-din na ma'aikatar, Kubra Imam ita ta jagoranci tawagar don kula da dawowar dalibai a zangon farko.

Tawagar ta samu rahoton cewa daliban ba su samu abincin dare na ranar Lahadi ba yayin da karin kumallon safe ma bai samu ba.

Kiru ya ce kwamishinan ilimi ya amince da tura Umar Sabo kwalejin yaren Faransa yayin da ya tura Isiyaku Abdullahi kwalejin yaren Sin da ke Kwankwaso.

Sanarwar Abba Kabir kan dakatarwar a Kano

Ya ce:

"Kwamishinan ilimi ya nuna bacin ransa kan wadannan shugabannin makarantun da irin halin da su ka nuna.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

"Ya umarce su da su mika duk wasu muhimman abubuwa a karkashinsu ga sabbin shugabanni.
"Ana bukatar su zuwa ma'aikatar ilimi da gaggawa har zuwa lokacin da za a kammala bincike."

Kwamishinan har ila yau, ya gargadi sauran shugabannin makarantu da su guji duk abin da zai kawo cikas ga wannan gwamnati na habaka harkar ilimi, cewar Vanguard.

Abba Kabir ya dakatar da shugabannin makarantu 3 a Kano

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantun sakandare uku saboda rashin zuwa wurin aiki.

Kwamishinan ilimi a jihar, Umar Haruna Doguwa shi ya ba da wannan umarni a yau Juma'a 21 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel