Tsadar Rayuwa: Abba Gida-Gida Ya Zabtare Kudin Makarantun Gaba Da Sakandare Da Kaso 50

Tsadar Rayuwa: Abba Gida-Gida Ya Zabtare Kudin Makarantun Gaba Da Sakandare Da Kaso 50

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umurnin rage kudaden makaratun gaba da sakandare na jihar
  • Wannan na cikin kokarin da gwamnatin Kano ke yi na ragewa al’umma radadin matsin rayuwa da ake ciki
  • Abba gida-gida ya bukaci shugabannin makarantun da su rage kudaden makaranta da kaso 50 cikin dari

Jihar Kano - A kokarin da ake yi na ragewa al'umma radadin halin da suke ciki na matsin rayuwa, gwamnatin jihar Kano ta ba da umurnin rage kudaden makarantun gaba da sakandare.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya umurci dukkanin shugabannin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakin jihar Kano da su rage kudaden da dalibai ke biya na makaranta da kaso 50 cikin dari.

Gwamnan Kano ya rage kudaden makarantun gaba da sakandare
Tsadar Rayuwa: Abba Gida-Gida Ya Zabtare Kudaden Makarantun Gaba Da Sakandare Da Kaso 50 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Dalilin rage kudin makarantar

Kara karanta wannan

Gwamna Yahaya Ya Ba Da Umarnin Rufe Gidajen Gala a Jiharsa, Ya Bayyana Dalili

Abba gida gida ya dauki wannan matakin ne da nufin ragewa iyaye nauyi a wannan lokaci da ake fuskantar matsi na tattalin arziki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku tuna cewa makarantun gaba da sakandare da dama suna kara kudin makaranta a yan baya-bayan nan saboda kalubalen da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Jerin makarantun da Abba Gida Gida ya nemi su rage kudinsu

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa makarantun da abun ya shafa sun hada da jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote (ADUST), Jami'ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK), da kwalejin Musulunci ta Aminu Kano (AKSIL).

Sauran sune Kwalejin kimiyya da fasaha ta Sa'adatu Rimi, Kwalejin karatun noma ta Audu Bako, da kwalejin KAS.

Ya rubuta a shafinsa na manhajar X:

"A wannan rana na samu ganawa da dukkanin shugabannin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakin jihar Kano inda na basu umarnin su rage kuɗaɗen da ɗalibai ke biya na makaranta kaso hamsin (50%) cikin ɗari sakamakon yanayin matsi da al'umma suke ciki.-AKY"

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Gwamnan Kano ya ware miliyan 700 don biyawa daliban BUK 7000 kudin makaranta

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kano ta amince da sakin kudi naira miliyan 700 domin biya wa dalibai 7,000 yan asalin jihar da ke karatu a jami'ar Bayero, BUK kudin makaranta.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel