Maiduguri
Sarki a Kudancin Najeriya ya ce jihar Borno domin jaje bayan ambaliyar ruwa. Gwamna Zulum ya mika godiya ga sarkin bisa jajen da ya musu kan jarrabawar.
Gwamna Farfesa Babagana Umaru Zulum ya kaddamar da fara taba kayan tallafi da kuɗaɗe ga waɗanda ibtila'in ambaliya ya shafa a Maiduguri, jihar Borno.
Shugaban rukunin kamfanonin BUA Group, Alhaji AbdulSamad Rabiu BUA ya bai wa waɗanda ambaliya ta shafa a jihar Borno tallafin N2bn na kudi da kayan abinci.
Rahoton da rundunar 'yan sandan jihar Borno ta fitar ya nuna cewa wasu mata hudu sun mutu a hatsarin kwale-kwale a yankin Bakassi, tsakanin Mafa da Dikwa.
Hukumar NDLEA ta kama abinci da magani da suka zama rubabbu bayan ambaliyar ruwa a kasuwannin Maiduguri. NDLEA ta ce kudin magani da abincin ya kai N5bn.
Wasu daga cikin wadanda ambaliyar Maiduguri ta shafa, sun koma kwana a cikin tantunan wucin gadi da suke kafawa a kan tituna. Sun ba da labarin halin da suke ciki.
Yan ta'adda sun jefa mazauna Damaturu da kewaye cikin duhu bayan sun lalata layin da ke samar masu wutar lantarki da ya taso daga Damaturu-Maiduguri.
Gwamnan jihar Neja, Muhammadu Umaru Bago ya bi sahun gwamnoni sama da 11, ya kai ziyarar jaje tare da ba da N250m ga waɗanda ambaliya ta shafa a Maiduguri.
A rahoton nan, za ku ji gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya jinjina wa dakarun rundunar sojan kasar nan saboda namijin kokarinsu wajen ceton rayukan jama'a.
Maiduguri
Samu kari