Labaran Duniya
Sherif Lawal ya fafata ne a filin dambe na J Hackney Leisure inda ya ji rauni a zagaye na hudu a karawarsa da Malam Varela; an tabbatar da mutuwarsa a asibiti.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya da Afrika, Aliko Dangote, shi ne na shida a jerin attajiran da suka fi kudi a masana’antar kere-kere. Ya doke attajirai 19.
Hukumar hana fasa kwauri ta ce ta damke lita 12,435 na man fetur wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 10.8 a hanyar Cameroon. An kuma kama jarka 61 a hanyar Benin.
Hukumar IMF ta nuna damuwa kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye inda ta ce hakan asara kawai zai jawowa Najeriya na biliyoyi.
'Yan jarida na taka rawa wajen samar da bayanai da rahotanni ga al'umma. Sai dai akwai kasashen da ba su da cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Akalla ma'aikata 200 ne ake fargabar za su rasa aiki a yayin da babban kamfanin kimiya na kasar Amurka, Microsoft, ya fara shirye-shiryen rufe ofishinsa na Najeriya.
Sojojin Nijar sun cafke kasurgumin dan bindigar nan na Najeriya, Kachallah Mai Daji a Illela a lokacin da yake yunkurin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar.
Sakamakon dumbin bashin Naira biliyan 132.2 da kuma yunkurin cimma bukatun gida, Najeriya ta takaita tura wutar lantarki zuwa zuwa Benin, Niger, da Togo.
Hizbullah ta harba rokoki ga Isra'ila bayan wani hari da Isra'ila ta kai a wani kauye da ke kudancin Lebanon a ranar Lahadi wanda ya yi silar mutuwar mutane da dama.
Labaran Duniya
Samu kari