Kamfanin 'WhatsApp' Zai Dakatar Da Wasu Wayoyi Daga Amfani Da Manhajar

Kamfanin 'WhatsApp' Zai Dakatar Da Wasu Wayoyi Daga Amfani Da Manhajar

  • Kamfanin 'WhatsApp' ya ce akwai wasu wayoyin 'Android' da IPhone da za su bar amfani da manhajar
  • Wannan doka za ta fara aiki ne a watan Oktoba da mu ke ciki inda za a lissafo wayoyin da abin ya shafa
  • A kwanakin baya, da aka sanar da doka irin wannan wanda kalolin wayoyi akalla 42 su ka samu matsala saboda haka

Manhajar 'WhatsApp' ya sanar da cewa zai tushe yin amfani da manhajar a wasu tsoffin wayoyi na 'Android'.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, Legit ta gano cewa wayoyin 'Android' masu girman 4.1 ko kasa za su bar amfani da manhajar.

Kamfanin 'WhatsApp' zai dakatar da wasu wayoyi wurin amfani da manhajar
Kamfanin 'WhatsApp' Zai Dakile Wasu Wayoyi Daga Watan Oktoba. Hoto: Ivan Pantic.
Asali: Facebook

Wasu wayoyi ne 'WhatsApp' zai dakatar?

Har ila yau, wayoyin iPhone da su ke amfani da iOS 11 suma za su bar amfani da manhajar.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin ya ce wayoyin 'Android' masu girman 5.1 ne kawai za su ci gaba da amfani da 'WhatsApp' daga ranar 24 ga watan Oktoba.

Wayoyin IPhone masu girman iOS 12 za su ci gaba da amfani da manhajar daga ranar 24 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta ce:

"Daga ranar 24 ga watan Oktoba, wayoyin 'Android' masu girman 5.1 ne kawai zuwa sama za su ci gaba da amfani da manhajar.
"Dole wayar ka ta karbi sakon karta kwana ko kira don tantancewa.
"Kafin dakatar da wayoyin za mu tura sakwannin gargadi a manhajar 'WhatsApp'.

Wasu wayoyi ne ake hasashen Whatsapp zai dakatar?

Yayin da kamfanin 'WhatsApp' bai lissafa wayoyin da za a dakatar daga amfani da manhajar ba.

Rahotanni na hasashen wayoyin LG da Sony da HTC da Motorola na daga cikin wadanda abin zai shafa.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

A bangaren IPhone Kuma dole ma su amfani da ita su kara girman wayar daga iOS 11 zuwa 12.

Masu amfani da 'Facebook' za su fara biyan kudi a wata

A wani labarin, Kamfanin Meta ya sanar da cewa masu amfani da Facebook da Instagram za su fara biyan kudi.

Kamfanin ya ce duk wasu masu amfani da manhajojin za su na biyan kudade kalilan duk wata.

Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg shi ya bayyana haka yayin wata ganawa ta musamman a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel