Kasar Faransa Na Rokon Morocco Kan Kin Karbar Tallafi Bayan Girgizar Kasa

Kasar Faransa Na Rokon Morocco Kan Kin Karbar Tallafi Bayan Girgizar Kasa

  • Alaka ta yi tsami tsakanin Faransa da Morocco tun bayan hadewar Faransa da Algeriya wanda ba sa ga maciji da Morocco
  • Yayin da girgizar kasa ta daidaita Morocco, kasar Faransa ta kawo tallafin Yuro miliyan biyar amma kasar ta ki karba
  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya roki Morocco da ta manta da siyasa ta karbi wannan kyauta ta tallafi da ta ke shirin ba ta

Marrakesh, Morocco – Yayin da kasar Morocco ke cikin wani hali bayan girgizar kasa, kasashe da dama na ba da na su gudumawa.

Kasar Faransa ma ba a barta a baya ba, ta yi kokarin kawo tallafi, amma kasar Morocco ta ki amincewa.

Faransa na rokon Morocco kan kudin tallafi da ta ba ta
Emmanuel Macron ya bukaci Morocco ta manta da siyasa. Hoto: Al-Jazeera.
Asali: UGC

Meye Faransa ke rokon Morocco a kai?

Wannan ne ya saka gwamnatin Faransa rokon Morocco da ta daure ta karbi wannan tallafi da ta ke kokarin bata yayin da aka rasa rayuka fiye da dubu uku a kasar.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilin Da Yasa Aka Kara Kudin Makaranta A Jami’ar BUK, Farfesa Sagir Abbas Ya Magantu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ya yi wannan roko inda ya ce ya kamata komai yanzu kam ya wuce a tsakani.

Macron ya ce ya kamata kasar ta gane cewa yanzu lokaci ne da ta ke bukatar taimako ba duba bangaren siyasa ba, cewar Al-Jazeera.

Ya ce akwai bukatar a mantawa da tsamin alaka a tsakani saboda wani dalili na siyasa, inda ya ce yanzu lokaci ne na jimami.

Ya kara da cewa gwamnatinsa na tare da kasar Morocco a ko wane lokaci kuma a shirye su ke su ba da duk wata gudumawa idan bukatan hakan ta taso, The Guardian ta tattaro.

Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta turo Yuro miliyan biyar ga Morocco amma mahukuntar kasar su ka ki karba da cewa idan dai daga Faransa ne ba sa bukata.

Kara karanta wannan

Lokacin da Aka Yi Alkawari Ya Wuce, Matatar Dangote Ba Ta Fara Aiki Ba

Alaka na kara rikirkicewa ne bayan Faransa na kara kusanci da Algeriya makwabciyar Morocco wanda ba sa jituwa da juna.

Ronaldo Ya Ba Da Otal Dinsa A Morocco Kan Girgizar Kasa

A wani labarin, Shahararren dan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo ya ba da gudumawar otal dinsa da ke Morocco don taimakawa mutane bayan girgizar kasa.

Ronaldo ya ba da otal dinsa mai suna Pestana CR7 saboda masauki ga wadanda iftila’in girgizar kasa ta shafa a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.