Akalla Mutum 8 Sun Rasu a Wani Hatsarin Jirgin Saman Soji a Kasar Kenya

Akalla Mutum 8 Sun Rasu a Wani Hatsarin Jirgin Saman Soji a Kasar Kenya

  • Wani jirgin saman sojin ƙasar Kenya mai saukar ungulu ya gamu da hatsari a kan iyaƙar ƙasar da ƙasar Somaliya
  • Rahotanni sun yi nuni da cewa aƙalla rayukan mutum takwas ne suka salwanta a hatsarin wanda ya auku da daddare
  • Ma'aikatar tsaro ta ƙasar ta tabbatar da aukuwar hatsarin inda ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin

Kasar Kenya - Hukumomi sun bayyana cewa aƙalla mutum takwas ne suka mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na soji a ƙasar Kenya a kusa da kan iyaka da ƙasar Somaliya.

Hukumomin kasar Kenya sun ce kawo yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa hatsarin ba wanda ya auku a gundumar Lamu da ke a gaɓar teku, cewar rahoton Africanews.

Kara karanta wannan

Karshen Yan Bindiga Ya Zo: Jihar Arewa Ta Dauki Wani Muhimmin Mataki Domin Murkushe Yan Bindiga

Jirgin saman soji ya yi hatsari a Kenya
Akalla mutane 8 ne suka rasa ransu a hatsarin Hoto: Tvcnews.com
Asali: UGC

Jami’an tsaro na gudanar da ayyukansu a yankin domin daƙile ayyukan ta'addancin ƙungiyar al-Shabab mai alaƙa da al-Qaida, wacce ke da sansaninta a ƙasar Somaliya kusa da kan iyaka.

Wane lokaci jirgin ya yi hatsari?

A cewar ma'aikatar tsaro (DoD), jirgin saman mai saukar ungulu ya yi hatsari a lokacin da yake sintiri da daddare, rahoton Aljazeera ya tabbatar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ma'aikatar ta ƙara da cewa, an kafa kwamitin bincike wanda aka tura zuwa wurin domin gano musabbabin hatsarin.

Rahotanni sun ce dukkanin sojoji da ma'aikatan da ke cikin jirgin sun mutu.

An yi ƙiyasin cewa aƙalla mutane takwas ne suka mutu amma ma'aikatar tsaron ta ce tana ta'aziyya ga iyalan matuƙan jirgin, inda ba ta ambaci ko mutum nawa suka rasa ransu ba.

Akwai sojojin a ƙasar Somaliya

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji da 'Yan Sanda Da Dama a Jihar APC

Akwai sojojin ƙasar Kenya a cikin ƙasar Somaliya a matsayin wani ɓangare na tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka domin taimakawa wajen yaki da kungiyar al-Shabab.

Dakarun na Kenya an tura su Somaliya a shekara ta 2011, sai dai, yanzu haka ana shirye-shiryen janye dakarun ƙasa da ƙasa yayin da sojojin Somaliya ke karɓar ragamar ayyukan tsaro.

Jirgin Sama Ya Yi Hatsari a Legas

A wani labarin kuma, an shiga tashin hankali bayan wani jirgin sama na kamfanin United Nigeria Airlines, ya gamu da hatsari a jihar Legas.

jirgin ya samu matsalar da ta kai ga sauka daga asalin titinsa na tashi ko sauka, lamarin da ya haifar da firgici da tashin hankali tsakanin Fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel