“Warin Jiki”: An Fatattaki Wani Mutum Da Iyalinsa Daga Jirgin Sama Saboda Fasinjoji Sun Ce Suna Wari

“Warin Jiki”: An Fatattaki Wani Mutum Da Iyalinsa Daga Jirgin Sama Saboda Fasinjoji Sun Ce Suna Wari

  • An bukaci wani fasinjan jirgin sama, Yossi Adler, matarsa, Jennie da diyarsu su fita daga wani jirgi bayan sauran fasinjoji sun yi korafi
  • An rahoto cewa an yi zargi mutumin da iyalinsa suna warin jiki wanda ya jefa sauran mutane cikin wani hali
  • Mutumin ya nuna fushinsa, cewa fasinjojin da jirgin na Amurka sun ci zarafinsa da iyalinsa

Wani mutumi mai suna Yossi Adler, matarsa Jennie da diyarsu sun shiga wani jirgin sama amma sai aka fatattake su bayan sauran fasinjoji sun yi korafin cewa suna mugun wari.

An fatattaki iyali saboda zargin suna wari
“Warin Jiki”: An Fatattaki Wani Mutum Da Iyalinsa Daga Jirgin Sama Saboda Fasinjoji Sun Ce Suna Wari Hoto: WPLG Local 10 News.
Asali: UGC

Mutumin ya koka cewa kamfanin jirgin bai yi masa da iyalinsa adalci ba kuma basu samu yin tafiyar yadda suka tsara ba.

Dalilin da yasa kamfanin jirgin Amurka ya fatattaki wani mutum da iyalinsa daga jirgi

Ya bayyana cewa an nuna musu wariya saboda addininsu don su Yahudawa ne, rahoton Daily Mirror.

Kara karanta wannan

"Sabuwa Fil a Leda": Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

WPLG Local 10 News ta nakalto yana cewa:

“Akwai wani dalili na addini da ya sa suka kore ni daga cikin jirgi, ba ma wari. Babu wanda ke da wari a nan, kwatsam, muna tashi, sai suka rufe kofar sai suka ce ka yi hakuri yallabai, wasu sun yi korafi cewa kana da warin jiki don haka ba za mu bari ka koma ba."

Kamfanin jirgin Amurka ya tabbatar da cewa an fatattaki ma'auratan da diyarsu daga jirgin amma sun ce an yi masu hayar wani jirgin. Kamfanin jirgin ya ce an tarairaye su da kyau sannan an basu tikitin abinci.

"An cire Mista Adler da matarsa daga jirgin sama lokacin da fasinjoji da dama suka yi korafi a kan warin jikinsu. An kama masu daki a otel don su kwana sannan an basu tikitin abinci. An sake kama masu wani jirgin a ranar Alhamis."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Ma'auratan sun ce sun fito daga jirgin sannan sun tambayi sauran mutane a filin jirgin ko da gaske suna wari.

Yar Najeriya Ta Mutu a Jirgin Egypt Air, An Yasar Da Gawarta a Alkahira

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta gamu da ajalinta. Matashiyar matar ta mutu ne a cikin jirgin sama na Egypt Air a hanyarta ta zuwa birnin Landan, kasar Birtaniya.

An rahoto cewa matashiyar wacce ba a bayyana sunayenta ba, ta baro Najeriya zuwa Landan a cikin jirgin Egpyt Air mai lamba MS 876 zuwa Alkahira a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagas lokacin da ta mutu a cikin jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng