Labaran Duniya
A yayin da aka yi ta yada jita-jitar barinsa duniya, Sarki Charles III wanda ke fama da cutar daji, ya bayyana a gaban bainar jama'a a ranar Talata.
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fitar da jerin kasashe 10 mafi arziki a Afirka da aka shiga shekarar 2024 tare da fitar da Najeriya daga jerin.
Bayan ɗage dukkanin takunkumi da kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, an ci gaba da kai wuta Nijar, mazauna kasar sun yi martani.
Najeriya ta ƙara samun daraja a ƙasashen da ke ta ƙarfin fasfo, wanda ke ba ƴan ƙasar wani tagomashi yayin tafiye-tafiye zuwa zuwa Iran, Kenya da wasu kasashe 43
Shugaban kasar Aljeriya ya kaddamar da wani katafaren masallaci a gabar tekun 'Bahar Rum' wanda ya zama mafi girma a Afrika kuma na uku mafi girma a duniya.
Binciken da Legit Hausa ta yi a shafin yanar gizon ECOWAS ya nuna cewa har yanzu kasashen uku na cikin jerin sunayen mambobin kungiyar, yanzu sun koma 15.
Alamu masu karfi na nuni da cewa kungiyar ECOWAS za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Burkina Faso, Mali da Nijar biyo bayan sauyin gwamnati a kasashen uku.
A tsawon lokaci, an samu wasu 'yan wasan kwallon kafa da aikata laifuka daban-daban a wajen wajen filin wasa kuma an yanke musu hukunci bisa doka.
An samu sauyi a jerin manyan masu kudin duniya a 2024 inda matsayin Elon Musk da Mark Zuckerberg suka sauya sannan biloniyan Faransa ya shige gaba.
Labaran Duniya
Samu kari