Labaran Duniya
Bayanai da suka fito daga fadar gidan sarautar Ingila sun nuna cewa Sarki Charles ya kamu da cutar daji. An gano hakan ne yayin masa maganin matsalar mafitsara.
'Yan sanda a Indiya sun tsare wani tantabara na tsawon wata takwas a hannunsu bisa zarginta da yi wa China leken asiri, daga bisani an saki tantabara bayan bincike.
An yi gwanjon lemo mai shekaru 285 da aka gano a bayan wata tsohuwar dirowar ajiyar kaya a kan $1,780 (kimanin naira miliyan 1.8) a Ingila, abun ya ba kowa mamaki.
Yan Afirka, Asiyawa, Turawa, da Amurkawa sun binciko wuraren yawon bude ido daban-daban, ga wasu jerin kasashe biyar da ya kamata ku ziyarta a shekarar 2024.
A wasu sassa na duniya kamar Norway, Kanada, da Finland, wani lamari mai ban sha'awa yana faruwa inda rana ke zuwa kusa da Da'irar Arctic, wanda ke sa ba ta faduwa.
A karon farko an dage zaben shugaban kasa a Senegal, Shugaba Sall ya sanar da hakan cikin jawabi da ya fitar inda ya ce bincikar wasu alkalai yasa ya dauki matakin.
Bernand Arnault ya zarce Elon Musk ya zama sabon wanda ya fi kowa kudi. A goman farko Forbes tace akwai Bill Gates, Mark Zuckerberg da Warren Buffet.
Lola Bowoto, wata 'yar Najeriya da ke karatu a jami'ar kasar Ingila, ta shiga shafukan sada zumunta inda ta nemi taimakon mutane domin ta biya ta kudin makaranta.
An kwantar da Sarkin Burtaniya, Charles III a wani asibitin kudi na Landan a ranar Juma'a don yi masa tiyata a mafitsara, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar.
Labaran Duniya
Samu kari