Labaran garkuwa da mutane
Zamfara - Yan bindigan da suka yi awon gaba da wasu malamai da ɗalibai a kwalejin koyar da aikin noma ta Zamfara sun nemi a hada musu miliyan N350m kudin fansa.
Zamfara - Gwamna Bello Matawalle ya ɗauki alkawarin kuɓutar da dalibai da kuma malaman da yan bindiga suka sace a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura.
Zamfara - Biyu daga cikin malamai da kuma wani ɗalibi ɗaya da yan bindiga suka sace a kwalejin noma dake Bakura, jihar Zamfara sun tsero sun koma makaranta.
Niger - Jami'an yan sanda a jihar Neja sun samu nasarar kubutar da shugaban jam'iyyar APC shiyyar C a Neja, wanda yan bindiga suka sace a kan hanyar zuwa gona.
Rundunar NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga da ke dauke da muggan makamai a hanyarsu ta zuwa wani gari watakila domin gudanar mummunan aikinsu ta fashi da makami.
Taraba - Wasu mazauna ƙauye a jihar Taraba sun fusata, inda suka yi gaba-da-gaba da yan bindigan da suka kawo musu hari domin satar mutane, sun kashe ɗaya.
Wasu yan fashi sun bi dare sun harbi tsohon kansila sannan suka yi awon gaba da matarsa da kuma ɗan jaririnta da bai wuce watanni 7 da zuwa duniya ba a Zamfara.
Yan fashin daji sun tare motar yan bikin aure inda suka tasa baki ɗaya waɗanda suke cikin motar zuwa cikin daji, amma jami'an tsaro sun ɗauki matakin gaggawa.
Labarin dake shigowa yanzun daga jihar Neja na nuna cewa wasu masu garkuwa sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar APC na shiyyar C, Aminu Bobi, da yammacin yau.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari