NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai a jihar Katsina

NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai a jihar Katsina

  • Jami'an NDLEA sun cafke wasu bata-gari dauke da muggan makamai a jihar Katsina
  • An kame su ne dauke muggan makamai da suka hada da AK-47 da sauran kayan laifi
  • A halin yanzu an mika 'yan ta'addan ga rundunar soji domin gudanar da bincike akansu

Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wasu mutane uku da ake zargi 'yan bindiga ne; Adamu Shehu, Tukur Mohammed da Ibrahim Suleiman yayin da suke kai farmaki a jihar Katsina, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, da sauran abubuwa masu hadari.

An kama wani mai kera makamai, Celestine Chidiebere Christian, tare da babban bindiga kirar G3 tare da alburusai 78 (RLA) mai girman 7.62mm da kuma harsasai guda biyar a jihar Benue yayin da suke kokarin tura makamin da alburusan zuwa Jos, Jihar Filato.

An yi kamen da kwato makaman ne a wuraren binciken ababen hawa na NDLEA a jihohin biyu, Daily Trust ta ruwaito.

NDLEA ta cafke wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai a jihar Katsina
Bindiga kirar AK-47 Hoto: GettyImages
Asali: UGC

Da yake magana yayin karbar makaman, Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya), ya shaida cewa NDLEA za ta ci gaba da tallafawa kokarin da sauran hukumomin tsaro musamman rundunonin soji ke yi na dawo da doka da oda a fadin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"A bangarenmu NDLEA, za mu ci gaba da yin iya kokarinmu tare da manyan jami'ai masu himma don dakile amfani da muggan kwayoyi a kungiyoyin masu laifi ta hanyar hana fataucin wadannan abubuwan da ke kawar hankali."

"Ta yin hakan, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ba da himma ga kokarin sauran hukumomin tsaro musamman sojojinmu a kokarin dawo da tsaro da kiyaye doka da oda a duk sassan kasar nan."

A wane yanki aka kame 'yan bindigan?

A cewarsa, jami'an NDLEA da ke sintiri a ranar Alhamis 5 ga Agusta, 2021 sun kama 'yan bindigar uku a karamar hukumar Malumfashi ta Katsina.

An bayyana cewa wadanda ake zargin suna kan hanyarsu daga karamar hukumar Igabi ta Kaduna ne zuwa karamar hukumar Kankara a Katsina.

Marwa ya ce an kwato motar Toyota Corolla mai lamba Kaduna TRK 149 AE, bindigogi AK-47 guda uku da alburusai, layu iri -iri, zobba, tsabar kudi da sauran kayayyaki.

Ya kuma ce tuni ya ba da umurnin a mika wadanda ake zargi ga rundunar soji da ke Katsina domin ci gaba da bincike.

Batun sace kwamishinan Neja: Gwamnati ba za ta tattauna da miyagu ko biyansu fansa ba

Iyalan kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun fara tattaunawa da wadanda suka sace kwamishinan, gwamnatin jihar ta ce.

Gwamnati ta kuma tabbatar da cewa wadanda suka sace kwamishinan sun tuntubi dangin inda a lokacin suka nemi N500m.

Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya fada wa THISDAY a wata hira ta wayar tarho jiya Laraba 11 ga watan Agusta cewa dangin ba za su iya biyan irin wadannan makudan kudaden da ake nema ba, “don haka suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen.”

Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai

A wani labarin, Kungiyar Daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana barayin da ke sace dalibai a yankin arewacin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya yi wannan kiran ne a madadin kungiyar a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.

Legit.ng ta tattaro cewa Asefon ya ce duk wanda ke da halin yin garkuwa da kashe dalibai to a bayyana shi a matsayin dan ta'adda kawai.

Ya yi Allah wadai da rufe wasu makarantu a wasu sassan arewacin kasar saboda karuwar satar dalibai, Nigerian Tribune ta kuma bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel