Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon da mutum 50, sun hallaka mutum 4 a Maradun
- A wani sabon harin 'yan bindiga, an yi awon gaba da wasu mutane sama da 50 a Maradun
- Rahoto ya bayyana cewa, an kuma hallaka wasu mutane 4 nan take a yayin harin na ranar Litinin
- Wasu rahotanni sun kuma bayyana cewa, mutane sama da 70 ne aka sace, amma 'yan sanda sun ce 50 ne
Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Litinin 23 ga watan Agusta ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka mutum hudu tare da yin awon gaba da wasu mutum 50 a garin Goran Namaye da ke karamar hukumar Maradun.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Muhammad Shehu, ya ce maharan, wadanda suka zo da yawansu, sun mamaye garin da tsakar daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu tare da sace wasu 50.
Amma, ya ce an tura jami'an 'yan sanda na dabaru zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, CP Yakubu Elkana ya ba da umarnin gudanar da bincike da ceto wadanda abin ya shafa cikin gaggawa.
PPRO ya ce CP ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu yayin da rundunar ke aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da doka da oda a yankin.
Jita-jitan cewa mutum sama da 70 aka sace, an kuma hallaka sama da 10
A bangare guda, majiyoyi sun bayyana cewa, akalla mutum 70 ne aka yi awon gaba dasu, yayin da aka hallaka sama da 10 nan take, in ji rahoton Premium Times.
Hamza Bakura, mazaunin garin Bakura, wanda ke kusa da Goran Namaye, ya ce an fara harin ne daga karfe 1 na dare.
A cewarsa:
“Nan da nan suka shiga kauyen, suka fara harbi amma akasarin mutanen da aka kashe yanka su aka yi, ba harbi ba."
Ya kara da cewa lokacin da jami'an tsaro suka isa kauyen da misalin karfe 4 na asuba, 'yan bindigar sun fafata da su.
Wata majiya da ke zaune a Talata Mafara, Mudassir Muhammad, ta kuma ce wadanda aka sace “sun fi 70”.
Ya kara da cewa:
“A cikin garinmu (a Mafara), sama da mutane 50 ne suka zo neman fakewa saboda harin. Abin takaici ne domin wasun su sun tako da kafa ne zuwa Mafara tun daga Gora da sassafe. Na tabbata kun san nisan dake tsakani."
A makon da ya gabata kadai, Yankofoji da Rini, dukkansu dake makwabtaka da Goran Namaye, 'yan bindigar da ake zargin yara ne ga Halilu Kachalla sun far musu, sun kuma tafka barna a cikinsu.
An kame wani saurayi da ya dirkawa budurwa ciki, ya kashe, ya binne ta a Adamawa
A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wani dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Mubi, Mumuni Abubakar, bisa zargin kashe budurwarsa mai juna biyu, Franca Elisha, tare da binne gawarta a cikin rami mara zurfi.
Rundunar ta kuma gurfanar da wasu abokansa biyu, Huzaifa Shuaibu da Rabiu Adamu, saboda rawar da suka taka dumu-dumu a lamarin, Punch ta ruwaito.
Franca Elisha, dalibar Diploma a Sashen Kimiyyar Laburare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Mubi, an binne ta a cikin rami mara zurfi bayan kokarin zubar da ciki da ta yi ya faskara.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce korafin da iyayen marigayiyar suka yi game da inda take ya kai ga binciken da ya gano yanayin da ke tattare da mutuwar ta.
Mumuni Abubakar, mazaunin Unguwar Sanda dake karamar hukumar Yola ta Arewa, ana zargin ya dirkawa Franca ciki, kuma da ta sanar da shi, sai ya dage cewa lallai ne ta cire cikin.
Asali: Legit.ng