Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga

  • Malamai biyu da kuma wani ɗalibi ɗaya da aka sace a kwalejin fasahar aikin noma dake Bakura sun tsero
  • Mataimakin shugaban makarantar, Ali Atiku, shine ya bayyana haka yayin fira da manema labarai yau Litinin
  • Yace hukumar makaranta ta gano cewa maharan sun yi awon gaba da ɗalibai 15 da kuma malamai guda uku

Zamfara - Malamai biyu da ɗalibi ɗaya daga cikin waɗanda aka sace a kwalejin noma dake Bakura, jihar Zamfara sun tsero daga hannun yan bindiga, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kwalejin, Ali Atiku, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin.

Malamai 2 da ɗalibi ɗaya sun tsero daga hannun Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Malamai da Dalibin Kwalejin Zamfara Sun tsero Daga Hannun Yan bindiga Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Atiku Yace:

"Biyu daga cikin malamai da kuma ɗalibi ɗaya sun tsero daga hannun yan bindiga bayan sun sace su, sun komo makaranta da safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

"Zuwa yanzun da nake magana da ku mun gano cewa maharan sun sace ɗalibai 15 duk maza, sai kuma malamai mata uku da namiji ɗaya, kuma sun kashe jami'an tsaron mu guda biyu."

Me hukumar yan sanda tace game da lamarin?

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ba tace uffan ba game da lamarin.

A baya, yan bindiga sun taba sace shugaban kwalejin aikin noma dake Bakura, Alhaji Habibu Mainasara.

Sai dai daga baya ɓarayin da suka yi garkuwa da shi sun sako shi bayan an biyasu kuɗin fansa, kamar yadda premium times ta ruwaito.

A wani labarin kuma Babu Wani Siddabaru da Muka Yi, Masari Ya Yi Magana Kan Raguwar Ayyukan Yan Bindiga

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Zamfara, sun kwashe dalibai, sun kashe yan sanda

Gwamna Aminu Bello Masari, yace sam babu wani siddabaru da gwamnatinsa ta yi wajen rage ayyukan yan bindiga a Katsina.

Masari ya bayyana cewa gudummuwa da kowa ke bayarwa a jihar kama daga sarakunan gargajiya, jami'an tsaro da masu ruwa da tsaki wajen nemo hanyar warware matsalar shine yake haifar da ɗa mai ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel