Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamnan Osun Zai Fara Biyan Sabon Albashin N75,000

Ma'aikata Za Su Warwasa, Gwamnan Osun Zai Fara Biyan Sabon Albashin N75,000

  • Gwamnatin jihar Osun karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta ce za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi a watan Disamba
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kolapo Alimi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 29 ga watan Nuwamba
  • Tun farko dai Gwamna Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a jihar Osun bayan an yi ta kai ruwa rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N75,000 ga ma’aikatan gwamnati a ranar 1 ga Disamba, 2024.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta haɗawa ma'aikatan da bashin wata ɗaya da suka biyo idan aka fara biyan sabon albashin.

Gwamna Ademola Adeleke.
Gwamnatin Osun za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi a watan Disamba Hoto: @Osun_State_Gov
Asali: Twitter

Gwamnan Osun zai fara biyan albashin N75,000

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnati na cikin alheri dumu dumu, gwamna ya fara biyan N72000

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne a wani taro da aka gudanar a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan Osun, Kola Adewusi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar manyan ƙusoshin gwamnatin Osun da wakilan ƴan kwadago ƙarƙashin jagorancin shugaban NLC na jihar, Kwamared Chris Arapasopo.

Gwamnatin Osun za ta biya bashin wata ɗaya

Da yake jawabi bayan taron, kwamishinan yaɗa labarai, Kolapo Alimi ya ce:

"Za mu fara biyan mafi karancin albashi na N75,000 a ranar 1 ga Disamba, 2024, kuma za mu biya bashin wata daya.”
“Wannan wani bangare ne na kudirin gwamnatin Gwamna Ademola Adeleke na inganta jin dadi da walwalar ma’aikata a jihar Osun."

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Adeleke ta nuna da gaske take yayin da ta zarce adadin N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar NLC ta sake jaddada cewa za ta fara yajin aiki a jihohin da suka gaza fara biyan sabon albashin daga ranar 1 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Edo: Gwamna ya taso hadiman magabacinsa a gaba, an ƙwato motoci 30

Gwamnan Kaduna ya fara biyan albashin N72,000

Rahoto ya gabata cewa gwamnatin Uba Sani ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashin N72,000 da ta yi wa ma'aikatan Kaduna alkawari a Oktoba.

Sanarwa daga babban mataimaki ga Gwamna Uba Sani kan sababbin kafofin sadarwa, ta ce an fara biyan kudin daga karshen Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262