Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Shugaban Jam'iyyar APC da Aka Sace
- Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta sanar da cewa jami'ai sun kuɓutar da shugaban APC da aka sace
- Kakakin yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, yace an gano, Aminu Bobi, ne a wani daji
- Hukumar ta yi kira ga mazauna jihar da su taimaka da bayanai domin kuɓutar da ɗaliban Islamiyyar Tegina
Niger - Rundunar yan sanda reshen jihar Neja ta tabbatar da nasarar kuɓutar da shugaban jam'iyyar APC shiyyar C, Aminu Bobi, daga hannun yan bindiga.
Kakakin rundunar na jihar, DSP Wasiu Abiodun, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Asabar, kamar yadda punch ta ruwaito.
Abiodun yace an kubutar da shugaban ne ranar Jumu'a da misalin karfe 3:30 na rana a dajin Igwamma, karamar hukumar Mariga, jihar Neja.
A jawabinsa, kakakin yan sandan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"An kuɓutar da wanda aka sace ne a daji, kuma a halin yanzu yana asibiti domin duba lafiyar shi, yayin da jami'ai ke cigaba da kokarin gano waɗanda suka sace shi."
Yaushe aka sace shugaban APC?
Abiodun ya kara da cewa a ranar 7 ga watan Agusta, wasu yan bindiga suka sace Bobi yayin da yake kan hanyar zuwa gona duba masu aiki.
Dailytrust ta ruwaito DSP Abiodun yace:
"A ranar 7 ga watan Agusta, wasu da ake zargin yan bindiga ne suka farmaki mutumin, Nasiru Bobi, tare da direbansa a kan hanyarsu ta zuwa gona a hanyar Ukuru, karamar hukumar Mariga."
"Maharan sun harbi direban motar a kafarsa kuma suka barshi anan yayin da suka yi awon gaba da shugaban na APC."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
A karshe jagoran APC, Asiwaju Tinubu ya yi magana, ya gode wa Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan
A cewar Abiodun, hukumar yan sanda ta tashi tawagar hadin guiwa da ta haɗa da yan sanda, sojoji da yan bijilanti zuwa yankin domin binciko ɓarayin.
Yace daga baya aka samu nasarar ceto direban, inda aka kaishi asibitin kwantagora domin samun kulawa ta musamman.
Hakazalika, kakakin yan sandan yace hukumarsu tana maraba da duk wani bayani da zai taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban Islamiyyar Salihu Tanko, Tagina, cikin koshin lafiya.
A wani labari na daban kuma fadar shugaban ƙasa ta bayyana abinda shugaba Buhari zai fara yi bayan dawowa daga Landan
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, zai fara karbar bayanai daga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo , da makusantansa bayan dawowarsa Najeriya.
Shugaba Buhari , ya diro Najeriya ranar Jumu'a da yamma a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe, Abuja.
Asali: Legit.ng